✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Borno ta kafa kwamitin bincike kan zargin lalata da ’yan mata a kurkuku

Sakamakon zargin da ake yi cewa wadansu jami’an kula da fursunoni suna lalata da mata a gidan kurkukun da ake kira Kurkukun Kare Kukanka (Madimum…

Sakamakon zargin da ake yi cewa wadansu jami’an kula da fursunoni suna lalata da mata a gidan kurkukun da ake kira Kurkukun Kare Kukanka (Madimum Prison) da ke Maiduguri, inda ake tilasta musu zubar da ciki, Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima, ya kafa kwamitin bincike mai mutum 10 don gano gaskiyar zargin.

Da yake jawabi lokacin da yake kaddamar da kwamitin, Gwamna Kashim Shettima, ya nuna bakin ciki da damuwarsa kan samun wannan labari, inda ya ce, “A gaskiya ban ji dadin samun wannan labari ba, domin ya kamata a ce su ne suke kula da rayuwa da mutuncin wadannan bayin Allah ta kowace fuska don gyara halayensu su fito da kyawawan halaye, amma ba a je a yi ta bata musu rayuwarsu ba. Kuma wannan cin mutunci ne kuma cin zarafin dan Adam ne yin lalata da yara, kuma a tilasta musu zubar da cikin, wanda ba za mu taba amincewa da shi ba. Don haka duk wanda aka kama da laifi, babu shakka zai fuskanci fushin hukuma. Dole ne mu yi kokarin dakile wannan mummunar dabi’a. Don haka na kafa wannan kwamiti mai wakilai 10 a karkashin jagorancin Kwamishinan Shari’a na Jiha, Barista Kaka Shehu Lawan, wanda zai binciko gaskiyar al’amarin tare da bayar da shawarwarin yadda za a bullo wa al’amarin, kuma na ba su mako guda su kammala rahotonsu su mika mana.’’

Da yake mayar da jawabi, Shugaban Kwamitin kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar, Barista Kaka Shehu Lawan, ya ce, za su yi iyakacin kokarinsu wajen binciko gaskiyar al’amarin tare da mika rahotonsu cikin mako guda da aka diba musu.

A karshen makon jiya ne wata kafar watsa labarai ta Intanet, ta buga labarin cewa jami’an kula da fursunoni a gidan fursunan na Madimum Prison da ke garin Maiduguri na yin lalata da ’yan matan da suke tsare da su, kuma suna tilasta musu zubar da cikin idan suka samu, abin da ya janyo hankalin gwamnatin jihar ta kafa wannan kwamiti na bincike.