Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Gwamnatin Buhari na ciyar da dalibai sama da miliyan 10 – A’isha Buhari

Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya A’isha Buhari ta ce Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin  Shugaba Muhammadu Buhari tana ciyar da daliban makarantun firamare sama da miliyan 10 a fadin kasar nan.

Hajiya A’isha Buhari wacce Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa, Misis Dolapo Osinbanjo ta wakilce ta, ta sanar da haka ne a jawabinta wajen gangamin yakin neman zaben Shugaba Buhari na mata da matasa na Shiyyar Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a Lafiya ta Jihar Nasarawa a ranar Talatar da ta gabata.

ADVERTISEMENT

Ta ce gwamnatin Shugaba Buhari ta cikin shirinta na ciyar da daliban makarantun firamare kyauta a fadin kasar nan har yanzu tana ci gaba da ciyar da daliban da kuma daukar nauyin kula da lafiyarsu da sauransu, sabanin yadda a cewarta lamarin yake a baya inda gwamnatocin PDP da suka shude suka yi watsi da harkokin yara.

Ta ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da shirin da inganta shi da sauran shirye-shiryen da za su ci gaba da kare hakkin kananan yara muddin al’ummar kasar nan suka sake zabar Shugaba Buhari a karo na biyu. Ta ce matan kasar nan da dama sun amfana sosai da gwamnatin Shugaba Buhari zuwa yanzu, a cewarta da dama cikinsu sun samu aiki da gwamnatoci a dukan matakai wadansu kuma sun samu jarin kudi da sauransu don bunkasa harkokin kasuwancinsu.

ADVERTISEMENT

Ta yi kira ga al’ummar Arewa ta Tsakiya da kasa baki daya su fito kwansu da kwarkwatarsu su sake zabar Shugaba Buhari don ba shi damar ci gaba da samar musu da ribar dimokuradiyya. Ta kuma shawarce su da su tabbatar sun tsaya sun kare kuri’unsu bayan sun kada har a gama kirga a bayyana sakamako. Ta kara da cewa idan da hali ma su tafi wajen zaben da abincinsu su tsaya har a gama komai a idanunsu, don kada a tafka magudi bayan zaben.

  Cincirindon yaqin neman zaven Shugaba Buhari na mata da matasa na yankin Arewa ta Tsakiya a Lafiya
Cincirindon yaqin neman zaven Shugaba Buhari na mata da matasa na yankin Arewa ta Tsakiya a Lafiya

Daga nan sai ta yaba wa Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaba Buhari na Mata da Matasa a Shiyyar Arewa ta Tsakiya da ta kunshi jihohin Filato da Kwara da Nasarawa da Benuwai da Taraba da Neja da Kogi da kuma Abuja, wanda ya shirya tare da gudanar da gangamin da dimbin magoya bayan jam’iyyar a kasa baki daya suka halarta. Ta bukace su da su cika alkawarin da suka yi na zabar dukan ’yan takarar APC daga sama har kasa.

Tun farko a jawabin Shugaban Kwamitin Yakin Zaben Shugaba Muhammadu Buhari na Matasa da Mata a Shiyyar Arewa ta Tsakiya, Alhaji Buba Marwa ya ce sun shirya gangamin ne don nema wa Shugaba Buhari da dukan sauran ’yan takarar Jam’iyyar APC a kasa baki daya nasara musamman a shiyyar. Ya ce tuni matasa da matan shiyyar baki daya suka sha alwashin yin dukan mai yiwuwa wajen tabbatar dukan ’yan takarar APC daga sama har kasa sun lashe zabubbukan da za a gudanar.