✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Filato ta dauki nauyin biya wa Musulmi 630 kudin kujerun Hajji

Gwamnatin Jihar Filato ta dauki nauyin biya wa Musulmi 630 kudin kujerun aikin Hajjin bana. Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Filato, Barista…

Gwamnatin Jihar Filato ta dauki nauyin biya wa Musulmi 630 kudin kujerun aikin Hajjin bana. Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Filato, Barista Auwal Abdullahi ne ya bayyana haka, lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos.

Ya ce bana alhazai 1,200 ne za su yi aikin Hajji daga Jihar Filato, inda ya kara da cewa ba a taba samun yawan alhazan da gwamnatin jihar ta biya wa kudaden kujeru kamar bana ba.

Har ila yau ya ce Gwamnatin Filato ta yi dukkan abubuwan da suka kamata, don ganin alhazan jihar sun ji dadin gudanar da aikin Hajjin bana.

SaI ya yi kira ga maniyyatan su kasance masu jin tsoron Allah, tare da bin abubuwan da shugabanni suka umarce su.