Search
Subscribe
Gwamnatin Filato za ta fara fitar da Dankalin Turawa zuwa kasashen waje

Gwamnatin Filato za ta fara fitar da Dankalin Turawa zuwa kasashen waje

Gwamnan Jihar Filato, Mista Simon Lalong ya ce Gwamnatin Tarayya ta amince wa gwamnatin jihar, ta fara fitar da Dankalin Turawa zuwa kasashen waje.                                                                                                                                                  Gwamnan ya bayyana haka ne kwanakin baya lokacin gabatar da dan takarar  Majalisar Dokokin Jihar a zaben cike-gurbi na mazabar Pengana a Karamar Hukumar Bassa a Jam’iyyar APC a zaben  da aka gudanar a makon jiya.

Ya ce an riga an ba mu izinin mu fara fitar da Dankalin Turawa zuwa kasashen waje daga Jihar Filato.  Don haka da yardar Allah a badi za a fata fitar da Dankalin Turawa zuwa waje daga Filato.

Ya ce akwai abubuwa da dama da aka  yi wa manoma a  jihar, don ganin an bunkasa harkokin noma.

“Mun farfado da kamfanin taki na Jihar Filato inda yake aikin samar da taki a farashin Naira 5,500 ga manoman jihar. Kuma mun bai wa manoma taraktocin noma a bana,” inji shi.

Gwamna Lalong, ya ce a lokacin da yake yakin neman zabe, ya yi  alkawarin idan aka zabe shi Gwamnan Jihar, zai sake dawo da babbar gonar kiwon kajin nan, mallakar Gwamnatin Jihar ta  BARC Farms  da ke garin Saya da aka sayar a shekarun baya.

Ya ce yanzu ya cika wannan alkawari domin ya sake sayo wa gwamnatin wannan  gona, don haka nan ba da dadewa ba za a sake farfado da gonar, domin ta ci gaba da aiki.

Ya ce babu idan al’ummar Jihar Filato suka rungumi aikin noma tattalin arzikin jihar da tattalin arzikin Najeriya  zai bunkasa.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin