✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Gombe ta rattaba hannu da Qatar don habaka ayyukan jinkai

Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan wata takardar yarjejeniya (MOU) da gidauniyar kasar Qatar don habaka ayyukan jinkai a daukacin Kananan Hukumomin Jihar 11.…

Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan wata takardar yarjejeniya (MOU) da gidauniyar kasar Qatar don habaka ayyukan jinkai a daukacin Kananan Hukumomin Jihar 11.

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, shi ne ya rattaba hannu a madadin gwamnatin Jihar Gombe, a lokacin da wakilin gidauniyar kasar Qatar din Mista Hamdi Mohammed, shi kuma ya sa hannu a madadin tawagar kasar Qatar. Batun hakan yana dauke ne a wata takarda mai dauke da sanya hannu babban mai taimakawa Gwamna na musamman kan harkokin yada labarai Isma’ila Uba Misilli.

Da yake jawabi Jim kadan, bayan rattaba hannu kan takardar a Gombe Hamdi Mohammed, cewa ya yi wannan gidauniya tana da burin fadada ayyukan jinkai a fadin Gombe da tallafin gwamna Inuwa Yahaya, na yadda yake samar da ayyukan raya kasa wa al’ummar sa.

Ya kara da cewa, a karon farko na wannan shirin Gidauniyar za ta tona rijiyoyin burtsatse da gina Masallatai da samar da sauran kayayyakin more rayuwa. Sannan ya ce za su haka rijiyoyin burtsatse 32 da Masallatai 11 a dukkan Kananan Hukumomi 11 na jihar kana daga bisani su mikawa gwamnatin Jihar, don mika su ga al’ummomin da zasu ci gajiyar. Wannan kason farko kenan na shirin inda a cewarsa za su tabo yankuna da dama in sha Allah. Daga nan sai ya kara da cewa a karkashin wannan shirin na jinkai za su haka rijiyoyin burtsatse da gina Makarantu da Asibitoci da Masallatai da gidan Marayu, inda tuni yanzu sun tona rijiyoyin burtsatse 1300 da gina Masallatai 400 a daukacin yankin Arewaci da Kudancin kasar nan, inda ya ce ayyukan su gaba daya gidauniyar ce ke daukar nauyin gudanar da su.