✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Gombe ta zargi PDP da zuga likitoci shiga yajin aiki

Gwamnatin Jihar Gombe ta bakin Kwamishinan Lafiya  Dokta Ahmed Muhammad Gana da na Watsa Labarai Alhaji Alhassan Kwami ta zargi ’ya’yan Jam’iyyar PDP da zuga…

Gwamnatin Jihar Gombe ta bakin Kwamishinan Lafiya  Dokta Ahmed Muhammad Gana da na Watsa Labarai Alhaji Alhassan Kwami ta zargi ’ya’yan Jam’iyyar PDP da zuga ’ya’yan Kungiyar Likitoci su shiga yajin aiki a jihar.

Da yake jan ragamar wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar a ranar Litinin kan yajin aikin na likitocin Kwamishinan Lafiya na Jihar Dokta Ahmed Muhammad Gana, ya ce ya san Gwamna Inuwa Yahaya mai kishin jiharsa ce da ya bai wa harkar lafiya kula ta musamman inda yanzu haka ake ta gine-gine a Asibitin Kwararru na Jihar don haka ba ya wasa da harkar kiwon lafiya. Ya ci gaba da cewa  ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne kawai suka zuga likitocin saboda rashin kishi.

Dokta Ahmed Gana, ya ce duk da likitocin sun ki sauraren gwamnati kan bukatun da suka gabatar wanda gwamnatin ta gaje su ne a baya, yanzu haka akwai wadansu likitoci masu kishi su 40 da suka ce ba za su shiga wannan yajin aikin ba, za su tsaya su taimaka wa marasa lafiya.

Ya ce tunda sun shiga yajin aiki, ba su da ikon da za su kori majinyata daga asibitocin gwamnati  tunda ba asibitocinsu ba ne. Ya ce haka   akwai ungozoma da sauran ma’aikatan jinya suna gudanar da ayyukansu baya ga manyan likitoci 40 da suka ki shiga yajin aikin wadanda suka  kira kansu  da Concern Doctors Forum.

Likitoci ’yan kasa da matakin albashi na 15 ne suka shiga yajin aikin saboda abin da suka kira kin kula da koke-kokensu na neman karin albashi da alawus-alawus da kuma kin biyansu albashi na tsawon wata 11.

Da manema labarai suka nemi jin ta bakin Shugaban Kungiyar Likitocin ta Kasa reshen Jihar Gombe, Dokta Sa’idu AB Alhassan,  ya ce saboda rashin kula da ake yi wa likitocin yanzu a cikin wata biyu likitoci 30 ne sun bar aiki a jihar suka koma wasu jihohi da kuma Asibiitin Koyarwa na Tarayya.

Dokta Sa’idu AB Alhassan, ya ce suna da sababbin likitoci da suka gama karatu ana biyansu albashi a kan matakin albashi na 7 tun lokacin da suke karatu alhali da suka gama ya kamata a kai su mataki na 10 amma ba a yi haka ba. Ya ce shi kansa a matsayinsa na Shugaban Kungiyar Likitocin shekara biyar bai samu karin girma ba.

Ya ce a duk fadin Jihar Gombe likitocin da ake da su ba su kai 300 ba, saura duk sun gudu sun nemi inda ya fi Gombe albashi mai kyau amma su da suka yi hakuri suka tsaya ba a kyautata musu.

Dokta Sa’idu ya musanta zargin da gwamnati take yi cewa ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne suka zuga su suka shiga yajin aikin, inda ya. ce ba gaskiya ba ce wannan zargi, su ’yan kasa ne masu kishi,  rashin biya musu bukatunsu ne ya sa suka tafi yajin aiki ba wasu dallai na siyasa ba.