✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Gombe za ta kashe Naira miliyan 110 don magance matsalar ruwan sha a jihar

Don shawo kan matsalar nan ta karancin ruwan sha da ta addabi al’ummar jihar Gombe, Gwamnan jihar Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ware tsabar kudi…

Don shawo kan matsalar nan ta karancin ruwan sha da ta addabi al’ummar jihar Gombe, Gwamnan jihar Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ware tsabar kudi har Naira miliyan 110 don shawo kan matsalar.

Matsalar tafi kamari a unguwannin Wuro-Juli da Tabra da Nayinawa da Kanoyel da Yankin Makarantar ‘yan mata ta Doma da kuma unguwar Federal low cost. Wannan batu yana dauke ne wata takarda mai dauke da sa hannun babban mai taimakawa gwamnan na musamman kan harkokin yada labarai Isma’ila Uba Misilli.

Gwamna Inuwa Yahaya, ya yi umurnin fara gudanar da aikin gyaran manyan bututun ruwan da suka dauko ruwan daga dam din Dadin-kowa suka kawo matattarar ruwan. Wadansu yankunann tun farko an yanke musu ruwan ne saboda sun ja ruwan ba bisa ka’ida ba kamar yadda Hukumar samar da ruwa ta jihar ta sanar.