Da Dumi Dumi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta bukaci a gurfanar da tsoffin gwamnonin jihar, a gaban kotu

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed
Gwamna Bala Mohammed ya jingine duk wasu ayyukansa

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya bukaci a gurfanar da tsoffin gwamnonin jihar, Isa Yuguda da Mohammed Abdullahi da kuma wasu mukarraban gwamnatocinsu a gaban kotu kan yin wawaso da dukiyar jihar. Wannan kira ya boyo bayan karbar rahoton na musamman da Kwamitin Gano Dukiyar Jihar Bauchi da aka Wawure ya gabatarwa gwamnan wanda kuma ya sami tsoffin gwamnonin da kuma wasu mukarrabansu da hannu dumu-dumu wajen wawashe dukiyar jihar da ta wuce naira Tiriliya daya a lokacin da suna kan mulki.

Bala Mohammed ya bada wannan umarnin ne bayan da ya karbi rahoton kwamitin da aka kafa  ranar 12 Juli na bara don ya binciko dukiyar jihar da aka karkatar a tsakanin shekarun 2007 zuwa 2019.

Gwmnan ya lashi takobin cewar duk wani jami’in gwamnati ciki har da tsofaffin gwamnonin jihar da kwamitin ya samu da laifi za a gabatar da su a gaban kotu. Sannan kuma ya umarci Alalin Klkalai na Jihar Bauchi da ya yi aiki kafada da kafada da kwamitin don tabbatar da an shirya tsaf do gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Da yake gabatar wa da gwamna rahoton kwamitin, Mukaddashin Shugaban Kwamitin, Janaral, Markus Koko Yake, mai murabus ya bayyana wa gwamna cewa wadannan dukiyoyi da kudi da kwamitin ya gano an yi babakerensu sun hada da kudaden tallafi na Paris Club da kudaden tallafi na ayyukan zaizayar kasa, da kudaden Hukumar Bada Ilimin Firamare na Baidaya da kudaden haraji da kuma wasu kudade da gwamnatocin da suka gabata suka ciwo bashin su amma aka karkatar da su.

Da muka tuntube shi don jin ta bakinsa, Mai Magana da yawun Tsohon Gwamna Abubakar Mohammed, Ali M. Ali cewa ya yi “Ba mu da labarin wannan sabuwar tatsuniyar da gwamna mai ci ya zo da ita don ya karkatar da hankalin jama’ar Jihar Bauchi daga badakalar da ake zarginsa da ita ta kwangila. Don haka da zarar na tuntubi maigidana zan sanar da ku abin da ya ce a kai.”

ADVERTISEMENT

A nasa bangare Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Gwamna Yuguda, Salisu Barau cewa ya yi maigidansa zai kalubalanci wannan rahoto da kwamitin ya gabatar don ya wanke sunansa.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya