✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jihar Bauchi ta gaza a shekara daya – Sakataren PDP

Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Bauchi ta nuna damuwarta bisa yadda gwamnatin APC ta shekara daya a kan mulki amma babu wani aiki kwaya…

Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Bauchi ta nuna damuwarta bisa yadda gwamnatin APC ta shekara daya a kan mulki amma babu wani aiki kwaya daya da za ta nuna ta kammala tun lokacin da ta karbi ragamar gwamnatin jihar.
Sabon Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP reshen Jihar Bauchi Alhaji Yayanuwa Zainabari ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce sama da kashi 85 cikin 100 na talakawan jihar ba su gamsu da yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da ayyukanta ba domin har yanzu akwai ma’aikatan da gwamnati ta tantance su amma ta gagara biyansu albashi na tsawon wata uku zuwa biyar. “Saboda haka Ranar Dimokuradiyya a Bauchi kamar ranar bakin ciki ne domin tun lokacin da APC ta kama mulki abin Naira 10 yanzu ya koma Naira 50, kayan abinci ya yi tsada, talauci ya addabi kusan kowa a Najeriya sun kuma gagara cika alkawuran da suka dauka a lokacin kamfen,” inji shi.
Zainabari ya kara da cewa akwai dimbin talakawa a Bauchi wadanda ba sa iya cin abinci sau uku a rana sakamakon yadda gwamnatin jihar take gana wa al’umma ukuba.
Sai dai kuma a zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke gidan gwamnati Kwamared Sabo Muhammed babban mai tallafa wa Gwamnan Jihar kan hulda da jama’a da kafafen watsa labarai ya ce gwamnatinsu ta yi kokari sosai a tsawon shekara daya da suka yi a kan mulki.