Search
Subscribe
Gwamnatin Jihar Gombe ki inganta makarantar nakasassu

Gwamnatin Jihar Gombe ki inganta makarantar nakasassu

Lokuta da dama, gwamnatoci a dukkan matakai kan ce suna kokari domin inganta harkar ilimi daga tushe, batun da ke zama tamkar waka, saboda alkawarin yakin neman zabe a Najeriya za a iya cewa bai sauya ba. A kullum ’yan siyasa alkawari suke na samar da ruwa, wutar lantarki, hanya, tsaro da uwa-uba ilimi wanda za a iya cewa shi ne na gaba wajen samar da duk wani ci gaba mai dorewa a duniya baki daya.

A yayin da gwamnatoci ke nuna bukatunsu na kawar da matslar barace-barace a cikin al’umma da galibi masu dauke da wata nakasa ake samu cikin harkokin barar, za a iya cewa a gefe guda gwamnatocin ba su shirya domin kawar da wannan matsala ba.

Jihar Gombe na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke da matsalar tattalin arziki in aka kwatanta ta da takwarorinta, wanda ya sanya ake samun mabarata wadanda wadansu ke da wata nakasa, walau ta makanta ko kurame ko guragu.

A fili yake cewa wadansu daga cikin wadanda ke shiga harkar bara suna yi ne a dalilai na dole sakamakon babu yadda suka iya, ba su da hanyar samun kudi ko wani tallafi na rayuwa da za su dogara da ita, kada a yi maganar samun  ilimi da zai taimaka musu a rayuwar baki daya.

Yanayin karatun nakasassu a Jihar Gombe da Najeriya na cikin mawuyacin hali. A Jihar Gombe, makaranta guda daya tak da ke koyar da nakasassu tana bukatar daukin gaggawa daga dukkan masu ruwa-da-tsaki a harkar ilimi.

Yanayin da makarantar ke ciki, wadda ita kadai ce makaranta ta gwamnati da ke koyar da wadannan bayin Allah babban abin takaici ne,  babu wadatattun dakunan karatu, domin wasu dakunan karatun da kwalaye aka raba tsakaninsu wanda ke sanya dalibai ba su fahimtar abin da malamai ke fadi a lokutan daukar darasi, maganganun dalibai na cin karo da juna.

A lokutan baya wadannan dalibai su ke fita da kansu domin neman ruwan da za su yi amfani da shi duk da cewa suna da matsala ta gani, hakan yana jefa rayuwarsu cikin hadarin gaske. Dakunan kwana da ke makarantar ba su wadaci dalibai ba, dalibin da ke da matsala ta gani, a zahirin gaskiya bai kyautu a ce yana tafiya mai nisa ba wajen zuwa makaranta. Ya kamata a ce gwamnati ta inganta dakunan kwanan daliban don kara ba su damar zama domin yin karatu.

Sau da dama a kasuwanni ko wuraren ibada akan samu makafin da ke bara ko neman taimako, inda wadansu makafin ke bayyana cewa su dalibai ne na wannan makaranta ta nakasassu, suna fita ne domin neman abinci da ya kamata a ce gwamnati ta samar musu kamar yadda ake samarwa a sauran makarantun kwana a fadin Jihar Gombe.

Batun tsaron lafiyar wadannan bayin Allah ma wani abu ne da ya kamata hukumomi su dauka da muhimmanci, ganin cewa wannan makaranta ta kurame da makafi da ke Jihar Gombe ba ta da cikakken tsaro, ba a kewaye ta da katanga ba kuma tana cikin jama’a ne inda a wasu lokuta akan samu batagari da ke shiga cikin makarantar.

Kungiyoyi da daidaikun mutane kan kai dauki wa daliban musamman na kayan amfani da suka hada da abinci da kayan rubutu da sauransu. Abin takaici shi ne zargin da ke fitowa daga wajen daliban na karkatar da kayan da wadansu ke bayarwa domin amfaninsu.

Dole hukumoni su tashi domin gudanar da bincike kan wannan zargi, in kuma ya tabbata gaskiya, a hukunta duk mai hannu wajen karkatar da su.

Ya kamata Gwamnatin Jihar Gombe a matakan da take dauka na inganta ilimi a jihar ta sanya makarantar nakasassun a sahun gaba. Ya kamata a duba yiwuwar samar da irin wadannan makarantu a kowace karamar hukuma da ke jihar sabanin guda daya da ke fadar jihar a yanzu.

Wani batu da ya kamata dukkan gwamnatoci su bai wa kula shi ne, kayan karatu da koyarwa na wadannan dalibai, lura da yadda suke da tsadar gaske. Misali keken rubutu na makafi yana da tsadar gaske ta yadda ba kowane dalibi ke da karfin mallaka ba. Wadansu na bada shawarar janye harajin da ke kan irin wadannan kaya domin ’yan kasuwa da ke shigo da su sayar da su a farashin da ba zai gagari masu bukata ba.

Lura da yadda ilimi ke kara bunkasa ta hanyar amfani da na’urar kwamfuta, manhajar da masu matsalar gani ke amfani da ita wajen karatu na da tsadar gaske wadda ke da wahalar samu. Ya kamata hukumar da ke lura da bunkasa fasahar watsa labarai na zamani ta kasa ta samar da hanyoyin samar da irin wadannan manhajoji a cikin gida Najeriya.

Babu wata hanya da gwamnatoci za su kawar da matsalar bara a Najeriya da ta wuce inganta rayuwar nakasassu, musamman harkar karatunsu.

Ya kyautu a ce yadda ake bai wa sauran bangarorin ilimi kula ta hanyar ware makudan kudi, a rika sanya makarantun nakasassu a ciki domin su ma su yi gogayya da sauran al’umma kamar yadda ake samu a kasashe da suka ci gaba.

Umar Ahmad Abubakar Umarun80@gmail.com (08039175742)

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin