✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi gargadi game da sabuwar cutar dabbobi

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kasance cikin shirin ko ta kwana sakamakon barkewar wata cutar dabbobi a…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kasance cikin shirin ko ta kwana sakamakon barkewar wata cutar dabbobi a Jamhuriyar  Nijar.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan Ma’aikatar Gona ta jihar, Hajiya Halima Lawal, ta yi kira ga masu kiwon dabbobi da mahauta da diloliý da direbobi da su rika lura da dabbobin da suke mu’amala da su.

“Akwai rahotanni da ke fitowa daga kasar Nijar wanda Hukumar Lafiya ta Dabbobi ta Duniya ta fitar inda take cewa an samu barkewar cutar mai suna Antrad a yankin Tillabery na kasar Nijar.

“Wannan cuta ta Antrad na da hatsari ga dabbobi da kuma dan Adam. ýCutar na iya rayuwa cikin kasa na tsawon shekaru su kuma dabbobi na kamuwa da cutar ne idan suka ci ciyawar da ta tsiro a kan kasar.

“Cutar ta kan iya sanadin kisan dabbobi masu yawa ta hanyar gurbata jinin dabbobin. A wasu lukutan cutar ta kan janyo kaikayi ga jikin dabbobi. Daga baya dobbobin da suka kamu da cutar za su fuskanci wahala wajen numfashi.

“Idan kuma aka yanka dabbobin sai ka ga jininsu ya yi baki nan take wanda hakan ya janyo aka samu sunan cutar Antrad,” inji ta.

Duk da ta bayyana cewa Jihar Kaduna ba ta da iyaka da kasar ta Nijar sai ta ce “Yanzu da muke cikin yanayi na tafiye-tafiye da dabbobi daga yankin  Sahel zuwa cikin kasar Najeriya hakan ne zai iya sa a samu bulluwar cutar a Jihar Kaduna.

“Gwamnatin Jihar Kaduna ta hannun Ma’aikatar Noma tuni ta tashi tsaye wajen ganin an sanya idanu matuka domin gano alamun cutar idan bukatar hakan ta taso. Sannan kuma likitocin dabbobi za su fara wayar wa da jama’a kai a kan alamun cutar da hanyayoyin kariya a duk fadin jihar,” inji ta.