✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta wa almajirai bara a titunan jihar

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar ta haramta wa almajiran makarantun allo bara a titunan jihar. Ya fadi haka ne…

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar ta haramta wa almajiran makarantun allo bara a titunan jihar. Ya fadi haka ne yayin bikin mika takardun daukar aikin malanta ga mutum 7,500 a birnin Kano.

Gwamna Ganduje ya ce gwamnati ta dauki matakin ne domin tabbatar da tsarinta na ba da ilimi kyauta kuma dole ga ’yan firamare da sakandare a fadin jihar.

Ya ce daga yanzu dole ne makarantun allo su shigar da darussan Ingilishi da Lissafi cikin tsarin koyarwarsu.

Gwamnan ya ce “Idan har kana zaton cewa ba za ka karbi tsarin namu ba, to sai dai ka bar jihar.” Gwamna Ganduje ya bayyana cewa daga yanzu duk yaron da aka kama yana bara to, za a kamo mahaifinsa ko mai kula da shi, kuma a gurfanar da shi gaban kotu saboda rashin mutunta dokokin jihar.

Ko a makon jiya ma sai da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga gwamnatoci da su rika kama duk mahaifin da aka samu dansa yana bara da sunan karatun Alkur’ani.

Bayanai sun nuna cewa akwai fiye da yara miliyan uku da ba sa zuwa makaranta, kuma mafi yawansu suna Arewa ne.

Sai dai almajirai ko mabarata sun yi watsi da dokar gwamnatin jihar, kamar yadda gidan rediyon BBC ya ruwaito. Ya ce da alama mabarata sun bijire wa matakin da gwamnatin Jihar Kano ta dauka na haramta bara a titunan jihar.

Gidan rediyon ya ce kwana guda bayan gwamnati ta haramta barar, ya zaga birnin Kano inda ya ga mabarata na ci gaba da barace-baracensu.