✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano na shirin mayar da Sarki Sunusi zuwa Bichi – Kungiya

Wata kungiya mai zaman kanta da ake kira ‘The Renaissance Coalition’ ta yi zargin cewa, yanzu haka gwamnatin jihar Kano na yunkurin musayar Mai Martaba…

Wata kungiya mai zaman kanta da ake kira ‘The Renaissance Coalition’ ta yi zargin cewa, yanzu haka gwamnatin jihar Kano na yunkurin musayar Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu zuwa masarautar Bichi.

A sanarwar da kakakin kungiyar Ibrahim A. Waiya, ya fitar ta bayyana cewar idan har Sarki Sanusi ya ki amincewa da sauyin da za a yi masa, gwamnatin za ta tube shi daga karagar mulki.

Kungiyar ta ce, wannan shirin yana zuwa ne a daidai lokacin da ake shari’a a kotu kan kalubalantar sabbin masarautu guda hudu da gwamnatin ta kirkiro a jihar.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da su janyo hankalin Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje wajen kauce wa abin da zai haifar da tashin hankali a jihar baki daya.

Sai dai da majiyarmu ta tuntubi Sakataren watsa labarai na Gwamna Abdullahi Ganduje, Alhaji Abba Anwar, Ya ce a bangaren gwamnatin jihar ba bu wannan shirin kuma ba su san wannan zancen ba.