✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta dauki malamai 600 don koyarwa a tsangaya

A kokarin Jihar Kano na tabbatar da almajiran makarantun tsangaya da na Islamiyya sun samu ilimin boko, gwamnatin jihar ta dauki malamai 600 da za…

A kokarin Jihar Kano na tabbatar da almajiran makarantun tsangaya da na Islamiyya sun samu ilimin boko, gwamnatin jihar ta dauki malamai 600 da za su koyar a makarantun tsangaya da ke jihar.

Sababbin malaman da gwamnatin ta dauka a karkashin shirin BESDA suna da  takardun shaida na NCE zuwa sama inda za su koyar da Ingilishi da Lissafi kafin a kara darussan Larabci da na addini da sauran darussan da ake koyarwa a firamare

Aminiya ta samu labarin cewa malaman za su koyar a ranakun Alhamis da Juma’a, kuma za su koyar daga karfe bakwai na safe zuwa biyar na yamma.

Da yake jawabi a lokacin taron rarraba takardun daukar aiki ga sababbin malaman Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje wanda Shugaban Ma’aiktan Jihar Kano Dokta Kabiru Shehu ya wakilta ya ce shirin wani bangare ne na shirin gwamnatin na bayar da ilimi kyauta kuma dole ga al’ummar jihar. “Wannan yana tabbatar da cewa gwamnati da gaske take game da shirinta na bayar da ilimi kyauta ga kowa.  Gwamnati a shirye take wajen tabbatar da samar da kayan aiki a makarantun jihar da suka kama daga makarantu firamare har zuwa karamar sakandare,” inji shi.

Gwamnan ya ce gwamnatin ta gama shiri tsaf don daukar karin malamai dubu uku don fadada shirin koyarwa a tsangayun.

A cewarsa gwamnatin ta kafa kwamitoci biyu da za su bibbiyi yiwuwa da dorewar shirin na koyarwa a makarantu tsangaya yadda za su sanar da gwamnati game da halin da shirin ke ciki.

A jawabin, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano Hajiya Lauratu Ado Diso ta bayyana cewa karkashin shirin za a bayar da takardar shaida ga daliban tsangaya a lokacin da suka kamamla karatu, inda kuma ta yi kira ga iyaye su tallafa wa shirin don kyautata rayuwar ’ya’yansu a nan gaba.