✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta koka a kan mayar da Kano Pillars garin Kaduna

A shekaranjiya Laraba ne gwmanatin Jihar Kano ta koka a kan yunkurin da Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta kasa NFF ta yi na dakatar…

A shekaranjiya Laraba ne gwmanatin Jihar Kano ta koka a kan yunkurin da Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta kasa NFF ta yi na dakatar da kulob din Kano Pillars daga cigaba da buga gasar rukunin Premier na Najeriya daga filin wasa na Sani Abacha da ke Kano zuwa Kaduna a sauran wasannin da suka ragewa kulob din a gasar.
Gwamnatin ta ce yin haka sam bai dace ba kuma wani yunkuri ne na dakile kulob din daga neman sake lashe gasar a karo na biyu a jere.
Bayanin haka na kunshe ne a lokacin da Mai ba Gwamnan Kano shawara na musamman a kan harkokin wasanni, Malam Ahmed Shu’aibu Gara Gombe ya bayyana wa wakilanmu haka a wayar tarho.
Malam Ahmed Shu’aibu ya ce kodayake magoya bayan kulob din sun yi kuskure na mamaye filin wasa a daidai minti na 87 bayan da dan kwallon Kano Pillars ya zura kwallo a ragar Enyimba a gasar rukunin Premier a karshen makon jiya, hukuncin da hukumar ta dauka a kan haka ba a yi wa kulob din adalci ba.
“Mayar da sauran wasanni zuwa Kaduna ko Legas gaskiya hukuncin ya yi tsauri”, inji shi.
Kwamitin shirya gasar Premier ta kasa (LMC) da Hukumar da ke kula da shirya wasan kwallon kafa ta kasa (NFF) sun bayar da sanarwar za a sake wasa a tsakanin Kano Pillars da Enyimba a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna a wani lokaci da za a ambata nan gaba.  Sannan hukumar ta ce za a sake wasan ne na tsawon minti 90 duk da cewa an dakatar da wasan farko a minti na 87 bayan da magoya bayan Pillars suka mamaye filin wasa a lokacin da suke murna da hakan ta sa ba a samu sukunin kammala saura mintuna uku a wasan ba.
Malam Ahmed Shu’aibu Gara-Gombe ya kara da cewa, bai kamata a sake wasan ba, idan ma ta kama za a sake yi a tsakanin kungiyoyin kwallon kafar biyu, to kamata ya yi a sake na ragowar minti ukun da suka rage ba daukacin minti 90 da hukumar ta nemi a sake ba.
Hukumar da ke shirya gasar rukuni ta kasa (LMC) da Hukumar shirya wasan kwallon kafa a Najeriya (NFF) sun ci tarar kulob din Kano Pillars da kuma dakatar da kulob din daga yin wasa a Kano ne bayan magoya bayan kulob din sun mamaye filin wasa na Sani Abacha da ke Kano a wasa da aka yi a tsakanin kulob din da na Enyimba Aba a lokacin da dan kwallon Pillars ya zura kwallo a daidai minti na 87 da hakan ta sa daukacin alkalan wasa da ’yan kwallon Enyimba suka bar filin ba tare da an kammala ba.
Yanzu hukumar ta mayar da wasan da za a sake yi a garin Kaduna bayan ta ci tarar kulob din makudan kudi don zama darasi.