✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Masar ta haramta kungiyar ’yan uwa Musulmi

Majalisar mulkin Masar ta umarci hukumomin kasar da su soke izinin zama kungiya ga kungiyar ’Yan uwa Musulmi, wadanda ke jerin kungiyoyin da ba ruwansu…

Majalisar mulkin Masar ta umarci hukumomin kasar da su soke izinin zama kungiya ga kungiyar ’Yan uwa Musulmi, wadanda ke jerin kungiyoyin da ba ruwansu da gwamnati da aka amince da su. Wannan kuw aya biyo baya umarnin hukumar shari’a, kamar yadda kafafen yada laba labaran kasar suka ruwaito.
An yi wannan yunkurin ne bayan da wata kotu a Masar ta haramta kungiyar ’Yan uwa Musulmi daga gudanar da harkokinta, sannan aka kwace dukiyarta, a daidai lokacin da akae kai wa ’yan kungiyar farmaki, bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Musulunci ta Shugaba Muhammad Mursi.
A hukuncin da aka yanke ranar 23 ga Satumbar bana, kotu ta haramta duk wata kungiya ko reshen ’yan uwa Musulmi.”
Shugaba Mursi, shi ne shugaban Masar na farko da aka taba zaba bisa tafarkin dimokuradiyya, amma shekara guda da ya shafe a kan karaga ta hadu da tarnaki, inda sojoji suka kifar da shi bayan ya ki jin kiraye-kirayen miliyoyin Misirawa, don haka aka kifar da gwamnatinsa a ranar 3 ga yulin bana. Kuma ranar 4 ga Nuwambar bana, za a fara tuhumar hambararren shugaba, Muhammad Mursi da laifin kisan kai.