✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Myammar ta haramta kungiyar addinin Buddha masu adawa da Musulmi

Wani kwamitin da Gwamnatin Myammar ta kafa don kula da harkokin limaman addinin Buddha, ya bayar da sanarwar haramta kungiyoyin da ke adawa da Musulmi,…

 ‘’Ya’yan kungiyar 969 da suka addabi Musulmi a MyammarWani kwamitin da Gwamnatin Myammar ta kafa don kula da harkokin limaman addinin Buddha, ya bayar da sanarwar haramta kungiyoyin da ke adawa da Musulmi, wadanda ke haifar da tashe-tashen hankula.
A kalla mutum 237 suka rasa rayukansu tun daga watan Yunin bara, inda mutum dubu 150 suka tafi gudun hijira. Wadanda aka fi cutarwa a daukacin rikicin Musulmi ne.
A sanarwar da aka bayar mai dauke da kwanan watan biyu da Satumbar bana, Kwamitin Sangha Maha Nayaka, kwamiti mai kula da harkokin limaman addinin Buddha, ya haramta wasu kungiyoyi daga cikin kungiyoyi 969.