✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Nasarawa ta kafa kwamiti don aiwatar da mafi karancin albashi

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya kafa kwamitin mutum 23  don duba batun aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu 30 a jihar.…

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya kafa kwamitin mutum 23  don duba batun aiwatar da mafi karancin albashi na Naira dubu 30 a jihar.

A lokacin da yake kaddamar da kwamitin a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lafiya, Gwamna Abdullahi Sule ya bukaci mambobin kwamitin su tabbatar sun gudanar da aikansu bisa tsarin ayyukan kwamitin don ganin sun samun nasara. Ya ce ba shakka tunda aka fara batun mafi karancin albashi na Naira dubu 30 gwamnatinsa ta yanke shawarar aiwatar da shi a jihar ba tare da bata lokaci ba don kara wa ma’aikatanta kwarin gwiwa don ba su damar ci gaba da bayar da cikakkiyar gudunmawa wajen ci gaban jihar.

Ya ci gaba da cewa, “Mun kuma sha alwashin bayar da fiffiko ga jin dadin ma’aikatanmu ne kasancewar suna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jihar musamman wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati a dukkan matakai.”

Daga nan sai Gwamnan ya ce a yayin gudanar da aikinsa, kwamitin zai yi la’akari da kudaden shigar jihar da kason da take samu daga Gwamnatin Tarayya da yanayin karfinta wajen biyan mafi karancin albashin da sauransu.

A lokacin da yake jawabi, Shugaban Kwamitin kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Dokta Emmanuel Akabe, ya tabbatar wa Gwamnan cewa kwamitin zai yi duk mai yiwuwa wajen gudanar da aikinsa yadda ya dace don kwalliya ta biya kudin sabulu.

Aminiya ta gano cewa daga cikin aikin kwamitin wanda aka ba shi mako uku, akwai samowa tare da bincikar kundin tsarin dokar mafi karancin albashi na kasa na shekarar 2009 da gyarar fuska da aka yi wa albashin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da irin yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta cimma da Kungiyar Kwadago ta Kasa don su yi koyi da hakan wajen aiwatar da shirin a jihar da sauransu.