✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Oyo ta dakatar da malamai kan karbar kudi daga dalibai

Gwamnatin Jihar Oyo ta bayar da umarnin dakatar da wadansu malaman makaranta 16 da ke koyarwa a makarantun firamare saboda zargin karbar kudi daga hannun…

Gwamnatin Jihar Oyo ta bayar da umarnin dakatar da wadansu malaman makaranta 16 da ke koyarwa a makarantun firamare saboda zargin karbar kudi daga hannun dalibai da kin bin umarnin canja musu wurin aiki.

Gwamnatin ta bayar da umarnin ne a ranar Litinin da ta gabata cikin bayanin da Shugaban Hukumar Ilimi Bai-Daya (SUBEB) Dokta Nureni Adeniran, ya yi a Ibadan.

Ya ce, ziyarar wasu makarantun firamare da ke Ibadan da ya jagoranta da kansa, ta sa gwamnati dakatar da malaman daga aiki, saboda bincike ya tabbatar da karbar na goro da malaman ke yi a makarantun.

Bayanin ya nuna cewa, akwai shugabannin makarantu da mataimakansu da malaman dakunan karatu a cikin wadanda dakatarwar ta shafa. Haka kuma Hukumar SUBEB, ta nada kwamitin ladabtarwa da zai yi binciken kwakwaf domin gano laifin da kowane malami ya aikata domin yi masa hukunci.

Dokta Adeniran, ya ce gwamnati ba za ta sanya ido tana kallon irin wannan mummunan aiki da malaman suke tafkawa ba tare da ladabtar da su ba. Irin wannan zagon kasa da wadansu mutane ke yi ga tsarin bayar da ilimin firamare mai inganci da gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Seyi Makinde ke yi alama ce da ke nuna rashin tausayi ga ’ya’yan talakawa da ake tatsar kudade daga hannun iyayensu.

Shugaban Hukumar SUBEB din wanda ya bayar da jerin sunayen malaman da aka dakatar da makarantunsu ya ce, “A lokacin da muka ziyarci makarantun ne muka gano gaskiyar zargin da ake yi wa malaman kan kin bin umarnin canja musu wurin aiki da karbar kudi daga hannun daliban firamare duk da shirin bayar da ilimin firamare kyauta da gwamnatin ta fito da shi a jihar.”

Cikin watan Mayun shekarar 2019 ne Gwamnatin Jihar Oyo ta bayar da sanarwar bayar da ilimin firamare da karamar sakandare kyauta a inda ta ware Naira miliyan 526 a matsayin somin-tabi na shekarar karatu ta farko wato 2019/2020. Ana sa ran makarantun za su bayar da sakamakon kudaden da suka kashe ga gwamnati a karshen kowace shekarar karatu.