Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Gwamnatin Oyo ta fitar da sabon tsarin hawa babur

Gwamnatin Oyo ta fitar da sabon tsarin hawa babur

Gwamnatin Jihar Oyo ta ce, ba za ta hana harkar sufurin ’yan acaba kamar yadda aka yi a Jihar Legas ba,  maimakon haka za ta bullo da sabon tsarin yin rajista da karbar katin shaida ga dukkan mutanen da suka mallaki babur na zaman kansu da na sana’ar acaba.

Sabon tsarin yana da nasaba da irin miyagun ayyukan da ake  zargin ana amfani da babur wajen aikatawa.

Da yake yi wa ’yan jarida bayani a Ibadan Kwamishinan Ayyuka da Sufuri Farfesa Raphael Afonja, ya ce “Rububin shigowa Jihar Oyo da wadansu ’yan acaba suka rika yi daga Legas kwanakin baya shi ya sa gwamnati ta rika daukar matakan tantance kowane dan acaba da za a tanadi katin shaida mai dauke da suna da adireshi da lambar BBN.” Ya ce, wannan tsari zai taimaka wajen kyautata tsaro da gano maboyar masu amfani da babur don aikata ta’asa a jihar. “Rahotannin kwacen jaka da wayoyin salula da harbin bindiga da masu amfani da babur ke aikatawa kamar yadda ya auku ga direban Kwamishinan Gidaje da Muhalli na Jihar da wadansu mutum biyu a kan babur suka harbe shi. Saboda aukuwar irin wadannan miyagun ayyuka ne ya sa muka bullo da sabon tsarin,” inji shi.

A binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa, kimanin kashi 45 cikin 100 na ’yan acaba a Jihar Oyo sun fito ne daga Arewa. Kuma mafi yawansu suna gudanar da ayyuka ne ba tare da sanin dokokin da mahukuntan jihar suke kafawa a kan ayyukansu ba. Haka kuma rashin jituwar da aka saba samu a tsakaninsu da fasinjoji a dalilin rashin jin harsunan juna da matsala tsakaninsu da jami’an tsaro sun taimaka wajen yawan tayar da jijiyar wuya da kame daga jami’an tsaro.

Wani dan acaba mai suna Tanko Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa: “Sau da yawa muna samun matsaloli ne saboda rashin shugabannin kungiya da za su rika tuntubar mahukunta suna sanar da mu halin da ake ciki. A wasu unguwannin da aka ga ya dace da samun shugabanni kuma mutanenmu ba sa girmamasu shi ne dalilin da ya sa muke zaune kara-zube ana wulakanta mu ba tare da mun iya kare kanmu ba. Muddin muka ci gaba da irin wannan zama dole ne a ci gaba da danne mana hakki. Ya kamata mu samar da shugabannin kungiyarmu a unguwanni daban-daban kuma mu rika yin taro a-kai-a-kai tare da girmama shugabanni kamar yadda sauran kabilu ke yi,” inji shi.

Shugaban Kungiyar ’Yan acaba ’yan Arewa a Jihar Oyo Malam Umar Muhammed Ganji, ya ce “Mun yi maraba da sabon tsarin da gwamnatin ta fito da shi a kan masu sana’ar acaba.”

Malam Umar ya ce tsarin yana da muhimmanci gare su wajen sanin matsayinsu da kare su daga masu aikata miyagun ayyuka tare da sanin irin gudunmawar da za su bayar ga kyautata tsaro da zamantakewarsu da jama’ar gari da jami’an tsaro.