Da Dumi Dumi

Gwamnatin Sakkwato ta fara mantawa da mu – ’Yan gudun hijira

‘Yan gudun hijira a bakin ajin makaranta, inda suke kwana

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yi kokari sosai har ta samu yabo daga ’yan gudun hijirar da suka baro kauyukansu sakamakon matsalar tsaro a yankunan, wadda ta yi sanadiyyar rasa dimbin dukiyoyi da rayuka.

’Yan gudun hijirar da suka baro mazaunansu don samun mafaka sama da shekara daya suna zaune ne a garin Gandi a Karamar Hukumar Rabah. A nan ne gwamnati da daidaikun jama’a suka rika tallafa musu da abinci, kafin samun mafitar da za ta mayar da su cikin walwala.

Aminiya ta ziyarci sansanin ’yan gudun hijira na garin Gandi domin sanin yanayin da suke ciki, musamman sakamakon yanayin damina da ya yi nisa da kuma ganin cewa dukkan mutanen manoma ne, shekara ta sake dawo masu amma ba zancen noma.

Malam Ciso Bagudu mai shekara 50, mai mata daya da ’ya’ya tara da jikoki 4 ya bayyana wa Aminiya yanayin da yake a sansanin, inda ya ce “Ina tare da iyalina a sansanin, amma wadanda suka girma sun je nema a Kurmi. A bana ban yi noma ba, gwamnatin jiha ta ba ni gona na yi noma amma lokacin da aka mika mini gonar, lokacin noma ya wuce. Kan haka ban shuka komai ba, amma ina yin noma a biya ni domin in sayi abin da za mu ci da iyalina a sansanin.”

Malama Zahra’u tsohuwa mai shekara 50 tare da mijinta da yaranta biyar take zaune a sansanin. Ta ce suna son gwamnati ta ba su wurin da za su zauna su bar makarantar firamaren da suke a cushe. Sun bukaci walwala da bai wa yara damar su yi karatu.

ADVERTISEMENT

“Komai ya birkice a sansanin, makewayinmu ya kazance. A ajin da muke kwana mu 50 ne a cikinsa manya, akwai inda ya fi haka. Ga mu wuri daya tare da surukanmu, ba maganar maza su tafi wajen matansu, domin ko sun tafi ba wurin shiga. Gwamanati ta yi alkawarin za ta ba mu wurin da za mu koma, ta zo ta ba mu. Idan haka bai samu ba, ta taimaka ta yi mana maganin barayin nan da aka ce har yanzu suna cikin dajin garinmu a Tabanni, domin mu koma ya fi mana nan,” inji Zahra’u.

Idrisa Sahabi mai shekara 35 da mata biyu da ’ya’ya bakwai, shi ma daga kauyen Tabbani cewa ya yi:  “Babu wani dadin rayuwa, babu abinci a sansaninmu. Tun Sallah Karama da aka kawo abincin nan ba a sake ba, sai a Sallah Babba aka kawo mana abincin Sallah, shi ke nan. Maza aiki suke tafiya na noma su samu abin da za su sayi gero a yi musu kunu ko tuwo, in ka samu sai ka bai wa iyalinka su gyara maka. Yanayin da muke ciki, idan zaman lafiya ya samu barin nan ya fi mana.

“Ina kira ga Gwamnan Jihar Sakkwato ya yi sulhu da mutanen nan kamar yadda na Zamfara ya yi, don mu gane inda aka dosa. A yanzu ba mu san inda aka fuskanta ba, an bar mu kara-zube. Fatarmu a samu zaman lafiya, domin duk abin da ka samu idan gidanka ba lafiya aikin banza ne. Abin da gwamnati ta yi mana mun ji dadi, ba mu raina ba,” inji shi

Jamilu Shehu Alikiru mai shekara 29, ya ce “Gwamnati na kokari gwargwado ba matsala, yanzu ne abin ya ja baya ba a samun abinci sau uku a yini, sai dai wadansu maza na fita lebaranci su ciyar da iyalansu.”

Ya ce kauyukan da ke kusa da Gandi duk sun koma gidajensu, wadanda ke sansanin ba su wuce mutanen Tabanni da Kursa da Rukunni da Dutsi ba, akalla akwai mutum 1000 maza da mata a sansanin.

“An fi wata biyar da yi mana alkawarin matsugunni, an ce mana nan ba da jimawa ba, amma shiru wadansu ma sun dauki hayar gidaje a Gandi domin zama da iyalansu. Ya kamata a zo a ba mu wuraren da tallafin da za mu gina gidajen, kamar yadda ta ba mu gona mu yi noma har zuwa yanzu muna jiran taki,” inji Alikiru.

Ya ce manyan ’yan kwamitin jiha sai su kwashe mako uku ba su je wurin ba. Asibitin kula da su ma ya dakatar da bayar da magani, jami’an lafiya sun watse. Abin dai ya yi kamar an gaji da su. Ya ce yana fata gwamnati ta ba su matsugunni don kowa ya huta.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin jagoran Kwamitin Gwamnatin Jihar, Malam Muhammad Lawal Maidoki kan al’amarin ’yan gudun hijirar amma abin ya ci tura, har zuwa hada labarin bai same shi ba.

Share