✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Sakkwato ta sallami masu sharar hanya 550

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sallami ma’aikata 550 masu sharar titi da tsabtace manyan hanyoyin birnin bisa zargin suna karbar albashi a  ma’aikatu biyu, kuma wadansu…

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sallami ma’aikata 550 masu sharar titi da tsabtace manyan hanyoyin birnin bisa zargin suna karbar albashi a  ma’aikatu biyu, kuma wadansu daga cikinsu ba su zuwa aiki.

Kwamishinan Muhalli na Jihar, Alhaji Sagir Attahiru Bafarawa ya shaida wa manema labarai cewa wadansu daga cikin masu sharar suna karbar albashi a kananan hukumominsu, wadansu kuma an cire su ne domin ba su zuwa aiki.

Alhaji Sagir Bafarawa ya ce sun yi haka ne domin tsabtace bangaren da kawo gyara, inda ya ce za a sake daukar sababbin masu sharar nan gaba kadan.

Daya  daga cikin wadanda aka sallama wanda ba ya so a ambaci sunansa ya ce bai san laifinsa ba, inda ya ce yana fitowa aiki kuma ba ya da wani wuri da yake karbar albashi. “Ban taba ganin haka ba, a sallame ka daga aiki ba wani laifin da ka yi. Ba a taba kiranka aka shaida maka ka yi laifi ba ballanta a gargade ka a baki ko a takarda. Kana aiki a kan ka’ida, an ba ka takardar kama aiki tsawon lokaci kawai gwamnati ta sallame ka kuma kana da iyali da ’yan uwa. Har yanzu da nake magana da kai ba a fada min laifina ba. Gaskiya an zalunce mu. Allah Ya kwato mana hakkinmu,” inji shi.

Wani ma daga cikin wadanda aka sallama da aka sakaya sunanasa ya ce, “Har yanzu ban san dalilin sallamarmu ba, ba wanda ya yi mana bayani. Yanzu an mayar da mu maso neman aiki. Gwamnatin da muka goyi bayan kafawa ce ta yi mana wannan cin zarafi, ba a kyauta ba.”

Wani mai fafutikar kare ’yancin dan Adama, Malam Mansur Isa Buhari, ya ce wannan lamarin ci baya ne ga samar da ci gaban jihar, inda ya ce duk laifin da ake ganin mutanen sun aikata ana iya ladabtar da su a dauki matakin da za su gyara. “Gwamnati ta zo tana gina wajenn zuba shara da kudin da ya fi wanda ake biyan albashin masu tsabtace garin. Gina jama’a ya fi gina wajen shara. Ina kira ga gwamnati ta dubi lamarin nan ta dawo da ma’aikatan,” inji Mansur Isah.