✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Shugaba Jonathan

Wai me ya sa kullum ba ka ganin kowace gwamnati a kasar nan da gashi? Me ya sa dukkan abin da muke karantawa daga rubuce-rubucenka,…

Wai me ya sa kullum ba ka ganin kowace gwamnati a kasar nan da gashi? Me ya sa dukkan abin da muke karantawa daga rubuce-rubucenka, ba mu ganin komai daga alkalaminka sai suka, sai kushewa, sai zagi a wasu lokuta? Me ya sa kullum kai a naka hange, gwamnatin Nijeriya ba ta iya ba, ba za ta iya ba? Me ya sa ba ka bar gwamnatin farar hula ko ta soja ba? Ba ka bar masu dukiya ko arziki ko talakawa ba? Me ya sa kai kamar yadda muke gani ba ka ganin komai sai kowa ba ya yin daidai a cikin gudanar da lamurran kasar nan?
Wadannan tambayoyi ne da nake tarawa a cikin kwamfuta daga masu biye da irin rubuce-rubucen da nake yi a jaridu da kuma intanet. A kodayaushe na sami lokaci nakan koma ga rubuce-rubucen nawa domin na ga wai shin da gaske ne, ni ido daya gare ni a lokacin da nake rubutu ko sharhi kan lamurran kasa ko mulki ko zamantakewa da makamantansu? Da gaske ne ni ina ganin gwamnatocin kasar nan ba su yin daidai daga tsare-tsaren mulkin da suke gudanarwa? Ko kuwa dai hakan ne ba sa yi wa al’ummar kasar abin da ya dace a harkar mulki ko tattalin arziki ko gudanar da zamantakewar rayuwarsu? Ban san amsar ba, domin ni ina ganin tamkar abin da jiki ne ya ji yake fassarawa, abin da kunne ne ya ji, yake karaswa, abin da idanu ne ya gani, yake nusarwa, to ina laifin yake?
Bari mu yi misali da wannan gwamnatin ta Shugaba Goodluck Ebele Jonathan, mu ga shin hangen Dala wai shiga birni ne? Shin abin da take fada game da ciyar da kasar nan gaba, hakan ne? Shin da gaske al’ummar kasar nan na cikin aljannar duniya ne daga tsare-tsaren gwamnatin a halin yanzu? Maimakon mu dubi komai da komai game da zaman dirshan din da gwamnatin ta yi na tsawon shekaru bari mu dauki bangare biyu kurum, na tsaron rayukan al’umma da kyautata jin dadin jama’ar kasar, mu ga ko jadawalin lissafin na bisa kan turba da alkalumma na gaskiya.
A cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya, babban kudirin da ke shimfide shi ne gwamnati ta tabbatar da tsaron lafiya da rayuka da kuma kyautata jin dadin al’ummar kasar. Wannan shi ne kowace gwamnati ya dace ta dasa a cikin kwakwalwarta domin a tabbatar da cewa ta kasance gwamnati ta-gari, mai kula da al’ummarta da kare su daga fadawa cikin rashin tsaro da kuma cire musu tsoro da samar musu da abubuwan more jin dadin rayuwa. Ke nan irin wannan gwamnati ita ce ake kira da gwamnatin jin dadin al’umma, gwamnati da ke damuwa da halin da al’ummarta ke ciki a duk rana ta Allah. Duk fadi-tashin irin wannan gwamnati na neman mafita ne daga halin da al’ummar kasar suka samu kansu; kama daga tsarin mulki da siyasa da tattalin arziki da sauran batutuwan jin dadin rayuwa.
Irin wannan gwamnati ita ce ake kira da Ingilishi ‘Welfare state’, gwamnatin dadadawa al’umma. Gwamnati da masana suka nuna cewa tana shiga cikin rauhin rayuwar al’ummar tata domin su san cewa suna da mai kula da su a duk rana ta Allah. Gwamnati ce da aka gina bisa tsarin samar da kyawawan al’amurran jin dadin rayuwa. Wato ke nan kamar yadda tsarin mulkin Nijeriya ya tanada, kamata ya yi a ce gwamnatin Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ta tanadi matakan da za ta bi domin ganin ta inganta zaman rayuwar al’ummar da take wa shugabanci. Amma tambayar da nake yi wa kaina a kullum ita ce, shin lallai kuwa wannan gwamnati ta san da wannan sashe na tsarin mulki da ya tanadi da ta tsare rayuka, ta cire tsoro, ta kuma samar da abubuwan  more rayuwa ga ilahirin al’ummarta?
Da yake ba ni ne Shugaba Jonathan ba, ba kuma ni ne mai ba shi shawara kan harkokin watsa labarai ba ko wani na kusa da shi, ba zan iya ba da amsa kai tsaye ba. Abin da zan yi shi ne in dora gwamnatin bisa silkelin da masana suka tanada na fahimtar ko gwamnatin na bisa turbar gaskiya ko kuma ta sanya giyar ribas ne wajen mulkin nata.
Shin gwamnatin Jonathan na kare rayukan al’ummar kasar nan kuwa? Mu dubi rayukan da aka rasa ta fuskoki da dama. Daga hannun ‘yan fashi da makami. Daga rikice-rikicen addini da na kabilanci. Daga hayaniyar ‘yan boko haram da Ombatse da ‘yan sara-suka da ‘yan daukar amarya da masu satar jama’a da kashe su don tsafe-tsafe. Shin aukuwar wadannan na nuna mana cewa akwai tsaro daga gwamnati? Shin wannan ba alama ba ce da ke nuna cewa jama’a yanzu na zama cikin tsoro ne, maimakon cikin tsaro? Shin fargaba da rashin zaman lafiya ba shi ne ke kai-kawo a tsakanin al’umma ba? To wai ina sashin tsarin mulki da ya ce a kare lafiya da rayukan al’umma? Kila an cire wannan sashe daga cikin tsarin mulkin Nijeriya da wannan gwamnati ke jagoranta!
Haka kuma wani bangare na tsarin mulkin da na ga kamar an yi watsi da shi, shi ne na daidaita rayuwar al’umma, a mayar da al’umma ta koma tamkar ‘ya’yan gurguzu, bai daya. Abin da aka yi wa Kudu, a yi wa Arewa, abin da aka yi wa Musulmi, a yi wa Kirista ko wanda ba shi da addini. A yi wa yaro da babba, a yi wa mace, a yi wa namiji. Ba bambanci! Amma shin hakan ne ke faruwa a cikin kasar a halin da muke ciki? Idan da gwamnati ta kokarta daidaitawa tsakanin al’umma da kila ba mu kasance cikin halin da muke ciki ba! dan Kudu na kyamar dan Arewa. Musulmi na nesa-nesa da Kirista ko marar addini. Igbo na kyamar Ijaw da sauran al’ummar Kudu-maso-Kudu. Yarbawa na ganin Hausawa a matsayin cima-zaune, kaskoki, su kuma suna ganin wadanda ba Hausa-Fulani ba, a matsayin baki. Maganar daidaito tuni ta kau, ana ta yakin juna cikin ruwan sanyi. A wannan badakala ina gwamnati, kuma me take yi?
Saboda haka idan muka ce gwamnatin yanzu ta gaza, ba wai don ba a son ta ba ne, sai dai don ta ki yin abin da ya dace a dube ta a matsayin gwamnatin kowa da kowa, ba ta ‘yan kalilan ba!
Gwamnatin da dukiyar kasa ba ta kasa ba ce, ta wasu ‘yan kalilan ce daga al’ummar kasar, ba gwamnati ba ce! Gwamnatin da ta kasa samar da al’amurran kare lafiyar al’ummarta, ai ba gwamnati ba ce! Gwamnatin da dukkan sassan gudanar da ilimin ‘ya’yanta ya durkushe, ba ta damu ba, ba ta kula ba, wannan ba gwamnati ba ce! Gwamnatin da talauci ya yi katutu tsakanin al’ummarta, wasu kuma ‘yan kalilan na kwance cikin tafkunan arziki, ba gwamnati ba ce! Ina mafita? Wannan kuma tambaya ce da ban san amsar ta ba! Amma ina da hasken da zan iya badawa, in an tambaye ni!