✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin ta kyauta da ta farfado da noman auduga – Manomi

Alhaji Abubakar Umar shi ne jami’i mai kula da noman auduga a Jihar Kebbi, kuma babban manomin audugar, a tattaunawarsa da Aminiya, ya ce shirin…

Alhaji Abubakar Umar shi ne jami’i mai kula da noman auduga a Jihar Kebbi, kuma babban manomin audugar, a tattaunawarsa da Aminiya, ya ce shirin Gwamnatin Tarayya na bayar da tallafi ga manoman auduga, zai farfado da noman auduga a Najeriya:

Me za ka ce kan shirin Gwamnatin Tarayya ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN), na bullo da shirin tallafa wa manoman auduga a Najeriya?

Kamar yadda aka sani a bana Gwamnatin Tarayya a karkashin kular Babban Bankin Najeriya (CBN) ta hanyar Kungiyar Masu Amfani da Auduga ta Kasa ta shigo ciki kan za ta ba da tallafi ga manoman auduga, domin ta ga alfanun abin a kan manoman shinkafa da aka bai wa tallafin gwamnati ta hannun Bankin CBN. Abin ya bunkasa noman shinkafa, ita ma auduga na da wannan bukatar. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wannan shiri a cikin watan Mayu, kuma gudunmawar ta shiga hannun manoman auduga, muna sa ran shirin zai samu nasara don za a habaka noman auduga a Najeriya.

To da wane lokaci ne auduga take yi?

Ita auduga ba kamar sauran abubuwa ba ne, da ba su yi in akwai karancin ruwan sama; irin su gero. Ana noman auduga da rani ta yi kyau kamar a cikin damina. Kowane lokaci auduga tana yi, ba sai da ruwan sama ba. Sai dai  nomanta a rani ya fi na damina wuya a bangaren ban-ruwa. Amma irin su daya ne da na damina da rani babu bambanci, kowane ka sanya zai yi, don ni na sha shuka irin damina a rani kuma ya yi lafiya lau babu wata tangarda.

An dade ana noman auduga a Najeriya, amma nomansa ya kasa bunkasa, wane alfanu yake da shi ga ’yan Najeriya da har sai Gwamnatin Tarayya ta yi masa shiri na musamman?

Lallai haka ne kamar yadda ka ce noman auduga tsohon lamari ne ana yin sa tun lokacin da ba a iya gurza audugar da inji. Iyayenmu shekara 50 da suka wuce, sukan gurza auduga su fitar da irinta daban ita daban, su markade ta, a yi sabi ta hanyar gargajiya. Daga baya-bayan nan ne kamar shekara goma sha da suka wuce, aka samu tabarbarewar noman, inda ya yi kasa, saboda matsalolin rashin samun iri ingantacce.

Bayan nan farashinta ya yi kasa, uwa uba ga rashin tallafi daga gwamnati, amma yanzu wannan gwamnati karkashin jagorancin, Shugaba Muhammadu Buhari, ta gano muhimmancin noman auduga da rawar da yake takawa a kasa, in aka yi la’akari da tun daga manomanta zuwa masu sarrafa ta da kai ta masaku, magurzar auduga daya na iya daukar mutum 500 aiki. In aka samar da magurza 30 a kasa ka lissafa ka gani can baya akwai masaka da yawa, amma da noman ya ja baya duk sun mutu, ba su wuce uku masu aiki yanzu ba. Da alama gwamnati ta sauya tunaninta ne, ta yi nazarin noman auduga na cikin lamarin da ke samar da abin yi ga matasa kuma hakan zai taimaki gwamnati a wannan bangare, don ba ta iya bai wa kowa aiki, samar da irin audugar ya nuna gwamnati ta fito sosai da nufin farfado da noman auduga.

Wane kira kake da shi ga gwamnati kan ta kara tsaya wa noman auduga?

Kirana ga gwamnati ta kara tsaya wa manoman auduga, hakan zai sanya a samu audugar ta yi yawa har a rika kai ta kasashen waje kamar a da. Kamar a baya can ko ba komai audugar Najeriya tana da kyau in akwai ta a kasuwa ba a barinta a dauki wata. Sannan duk abin da ake nomawa ba wanda ya yi darajar auduga, don ita kadai ce manominta ba ya zuwa talla har gida ake samunsa a saya, ba wani bata lokaci mai saye ba ya damuwa da nisan wuri. Kuma ko shekara nawa aka ajiye ta ba ta lalacewa.  Ya kamata a karfafa a rika noma abin da aka gada kaka da kakanni. Bayan man fetur, ba a bin da ya kai auduga kawo kudi.

Abin da ya sanya muka kara jin dadi ga wannan shirin kan farfado da noman auduga a Najeriya, ba wani manomi da ba zai yi maraba da shirin ba, don taimakon kasa ce.

Ko Gwamnatin Tarayya ta turo muku irin auduga da taki da magungunan kashe kwari a nan Jihar Kebbi?

Lallai Gwamnatin Tarayya, karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Babban Bankin Najeriya, sun turo wa manoman auduga da taki buhu dubu 77 inda kowane manomi zai samu buhun taki bakwai da irin auduga da kuma maganin kashe haki da maganin kwari, kuma a nan Jihar Kebbi mu ne na biyu wajen noman auduga; muna da manoman auduga dubu 11, inda Jihar Katsina ce ta daya ga noman auduga a Najeriya.

Amma da yardar Allah, in Allah Ya kai mu badi manoman auduga a Jihar Kebbi, sai mun kai dubu 15, saboda yadda jama’a suka karbi wannan shiri na noman auduga a nan jihar.

Muna godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, kan farfado da wannan shiri na noman auduga a duk fadin kasar nan.