✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta fara feshin kashe tsuntsaye masu bata kayan gona a Arewa maso Gabas

Gwamnatin Tarayya ta fara feshin magungunan kashe tsuntsayen da suka addabi gonakin jama’ar Arewa maso Gabas inda wani ma’aikacin Ma’aikatar Gona  da Raya Karkara ya…

Gwamnatin Tarayya ta fara feshin magungunan kashe tsuntsayen da suka addabi gonakin jama’ar Arewa maso Gabas inda wani ma’aikacin Ma’aikatar Gona  da Raya Karkara ya tabbatar da haka.

Shugaban ofishin feshi da tafiyar da harkar dabbobi na jihohin Adamawa da Taraba, Malam Adamu Kazaure, ya tabbatar wa manema labarai wannan yunkuri.

Ya ce an yi haka ne domin a rage asarar albarkatun gona da tsuntsayen ke janyowa a wannan bangaren kasa.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta samu rahotonnin bullar tsuntsayen; inda suke illa ga gonakin shinkafa a Arewa maso Gabas.

Ya ce jihohin Adamawa da Taraba ne abin ya fi shafa inda hakan ya sanya aka yi wannan feshin domin samun saukin lamarin.

Shugaban ya ce akalla kananan hukumomi 12 abin ya shafa a Jihar Taraba da suka hada da Lau da Donga da Bali da Ardo-Kola da Gassol da Karim Lamido da Ibbi da Wukari da sauransu. Sa’annan ya ce a Jihar Adamawa, kananan hukumomi hudu ne abin ya shafa da suka hada da Guyuk da Girei da Yola ta Gabas da Yola ta Arewa.

Kazauren, ya ce kananan hukumomin Lamurde da Numan da Demsa da kuma Shelleng suma za a musu riga-kafin wannan feshin nan ba da dadewa ba.

Ya ce idan aka kammala feshin, a jihar Adamawa, za a tabo jihar Bauchi da Yobe da kuma Gombe domin kashe wadannan tsuntsayen dake raunana albarkatun gonaki.