✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta fara raba wa ‘yan kasuwa dubu 30 rancen kudi a Nasarawa

Gwamnatin Tarayya ta fara raba wa kimanin ‘yan kasuwa dubu 30 rancen kudi a Jihar Nasarawa. A jawabinta jim kadan da fara raba wa ‘yan…

Gwamnatin Tarayya ta fara raba wa kimanin ‘yan kasuwa dubu 30 rancen kudi a Jihar Nasarawa.

A jawabinta jim kadan da fara raba wa ‘yan kasuwa kudi a babbar kasuwar zamani dake Lafiya shugabar hukumar tallafawa ‘yan kasuwa Misis Chinyere Okoracha ta ce, sun kasance a garin Lafiya babban birnin jihar ne don su fara raba wa ‘yan kasuwar rancen kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi alkawari.

Ta ce Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari an ware kimanin naira dubu 300 ne don rabawa ‘yan kasuwa a fadin kasar nan baki daya. Kuma a cewarta gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauki matakin ne don tallafi tare da inganta harkokin ‘yan kasuwa a kasar nan baki daya don su rika dogara da kansu.

Ta ci gaba da bayyana cewa “Kawo yanzu mun raba wa jihohi 15 rancen kudin inda muka bai wa kowane dan kasuwa Naira dubu goma. Sannan muka kasance anan jihar Nasarawa yau don mu ci gaba. Zamu bai wa ‘yan kasuwa dubu 30 a jihar nan daga yanzu zuwa karshen kwanaki 5 da zamu yi.”

Ta kara da cewa bayan an bai wa kowanna dan kasuwar Naira dubu goma zai biya kudin ne a cikin watanni 6. Wakilinmu ya zanta da wasu daga cikin ‘yan kasuwar da suka amfana da shirin inda duk suka yaba wa gwamnatin tarayya dangane da hangan nesa da tayi na karamcin inda suka ce ba shakka kudin zai taimaka musu wajen inganta harkokin kasuwancinsu.

Sun kuma bukaci gwamnati ta tabbatar da dorewar shirin. Daga nan sai suka yi kira ga sauran gwamnatocin kasar nan a duka matakai su yi koyi da Gwamnatin Tarayya musamman a bangaren don agaza wa marasa galihu cikin al’umma.