✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin tarayya ta tsawaita dokar kulle a Kano

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tsawaita dokar kulle  zuwa mako biyu  a jihar Kano, inda ta umarci jami’an tsaro da su tabbatar ana bin dokar sauda…

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tsawaita dokar kulle  zuwa mako biyu  a jihar Kano, inda ta umarci jami’an tsaro da su tabbatar ana bin dokar sauda kafa.

Ta kuma umarci jami’an tsaro da su tabbatar ana bin dokar hana fita a daukacin kasar daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe, tare da dokar hana zirga zirgar jama’a a tsakanin jihohi, da kuma dokar sanya takunkumin rufe baki da hanci a wuraren taruwar jama’a domin hana yaduwar cutar COVID-19.

Haka zalika gwamnatin ta tsawaita sassauta dokar kullen da ta yi a jihohin Legas da Ogun da Yankin Babban Birnin Tarayya da mako biyu, inda ta bukaci jami’an tsaro su tabbatar ana bin matakan kariya da aka ayyana tun da fari domin guje wa yaduwar annobar.

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 da shugaban kasa ya kafa, Boss Mustapha, ya sanar da haka ranar Litinin a Abuja, a jawabin da ya gabatar wa al’umar kasar a karo na 33 a kan annobar.

A ranar 27 ga watan Afrilu ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana dokar kulle ta tsawon mako biyu a jihar Kano.

A cewar Boss Mustapha, matakin tsawaita dokar kullen a Kano ya zama dole, domin sassautata ta ka iya jefa al’ummar Najeriya cikin mummunan hatsari.

A baya dai gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa za a iya sassauta dokar idan al’ummar jihar na bin matakan kariya sau da kafa.