✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya za ta kafa masaka a Jihar Katsina

Minista a Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari, Hajiya Maryam Yalwaji Katagum ta ce, Gwamnatin Tarayya za ta kafa masaka a garin Funtuwa da…

Minista a Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari, Hajiya Maryam Yalwaji Katagum ta ce, Gwamnatin Tarayya za ta kafa masaka a garin Funtuwa da ke Jihar Katsina. Ministar ta bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata a wata ganawa da ta yi da jami’an Gwamnatin Jihar Katsina, a karkashin jagorancin Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji  Mannir Yakubu.

Ministar ta ce hakan zai samar da ci gaba musamman ta fuskar kasuwanci da kuma zuba jari daga ’yan kasuwa na cikin gida da na ketare, ta hanyar kafa masana’antun.

Minista Maryam Katagum  ta bayyana irin dangantakar da ke tsakanin ma’aiktarta da Gwamnatin Jihar Katsina, inda ta ce daga cikin abubuwan da za su duba a jihar har da irin tanadin wuraren da gwamnati ta yi musamman a garin Funtuwa don assasa masana’antu a yankin. Hajiya Maryam Katagum ta kara da cewa za su kai ziyara wajen da gwamnatin ta samar domin gane wa idanunsu abubuwan da suke kasa da suka hada da wutar lantarki da hanyoyin sufuri. “A cikin wannan tattaunawa da muka yi, mun yi bayani kan tsarin aikin da za mu yi, ba wai duba wuri kawai ba, za mu rika tuntuba domin yin abin da ya kamata da kuma kyakyyawan nazari a kan wannan aiki. Muna bukatar shigowar masu ruwa-da-tsaki a cikin wannan shiri, wanda hakan ne zai bai wa masu zuba jari damar zuwa jihar don zuba jari,” inji ta.

Ta kara da cewa, sun amince za su ziyarci wannan katafaren fili da Gwamnatin Jihar Katsina ta samar domin kafa masana’antu a garin  Funtuwa.

A jawabin Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Mannir Yakubu ya bada tabbacin goyon bayan Gwamnatin Aminu Bello Masari a kan wannan shiri, inda ya ce gwamnatin ta shirya tsaf domin bada duk wata gudunmawar da ake bukata.

Ya kara da cewa, sun ji dadi matuka dangane da wannan tattaunawa da suka yi da Ministar, inda ya ce, “Wannan ne karo na farko da muka taba ganawa da wata minista har na tsawon awa biyu muna tattauna muhimman abubuwa da suka shafi Jihar Katsina. Mu ne muka fara kai ziyara har ofishinki, amma tun daga wancan lokacin babu wani abin da ya faru sai bayan wata shida, amma sai ga shi yanzu mun fara wannan aiki da zai canja yanayin tafiyar tattalin arzikin jiharmu. Muna fatar cewa  masakar wadda Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa ta za ta zama mai amfani a gare mu.” Mataimakin Gwamnan ya ce, Gwamna Masari ya amince da bayar da fili kadada 140 domin gudanar da wannan aikin na gina masaka a Funtuwa. Ya kuma kara da cewa, sai daga baya suka lura cewa wannan aikin yana bukatar babban fili wanda yanzu haka an kara mika bukatar samar da karin fili, kuma akwai fatar za a samu wannan kari.

Mataimakin Gwamnan har wa yau, ya gode wa Ministar da ’yan rakiyarta bisa nuna damuwa da Jihar Katsina da kuma wannan muhimmin aiki da suka sa a gaba na samar da wannan katafariyar masaka a garin Funtuwa wadda ya ce da yardar Allah cikin karamin lokaci an yi abubuwa da dama.

Daga cikin ziyarar aikin da  Ministar ta kai Jihar Katsina har da bude ofishin koyar da sana’o’i da aka gina a garin Dandagoro da ke Karamar Hukumar Batagarawa wanda ke karkashin ma’aikatarta. An gina wannan ofishi ne don koyar da sana’o’i wanda hakan zai rage zaman kashe wando tare da habaka tattalin arzikin al’ummar jihar. Bikin bude ofishin ya samu halartar masu ruwa-da-tsaki kan abin da ya shafi sana’o’i da kasuwanci gami da zuba jari.