✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarrayya ta ba manoman shinkafa bashi a Taraba

Mamonan shinkafa dubu 120 aka raba wa kayan aikin noma da bashin kudi domin gudanar da noman shinkafa a Jihar Taraba. Bashin wanda gwamnatin Tarrayya…

Mamonan shinkafa dubu 120 aka raba wa kayan aikin noma da bashin kudi domin gudanar da noman shinkafa a Jihar Taraba.

Bashin wanda gwamnatin Tarrayya ta bayar da  lamuni ta karkashin babban bankin Najeriya, watau CBN, an bayar da shi da nufin kara bunkasa noman shinkafa a Jihar.

Da yake raba kayayyakin aikin noma ga manoman shinkafar a Jalingo a ranar Talata makon jiya, shugaban kungiyar masu noman shinkafa ta kasa reshen jihar Taraba, Mallam Tanko Bobbo Andami, ya bayyana cewa gwamnatin Tarrayya ta bullo da shirin baiwa manoman shinkafar bashin, da zummar karfafa gwuiwarsu, wajen noma shinkafar da za ta wadata kasa  a maimakon dogara da wadda ake shigowa da ita daga kasashen waje.

Yace jihar Taraba na daya daga cikin jihohin da ake moma shinkafa mai yawa shi ya sa gwamnatin Tarrayya ta mai da hankali wajen tallafawa manoman shinkafa da bashi a Jihar.

Mallam Tanko Bobbo Andami ya kara da cewa jihar ta Taraba tana da manyan koguna wadanda suka ratsa sassan Jihar daban daban, hakan ya baiwa manoman damar noma shinkafar rani da damina a Jihar.

Yace kayan noman da kowanne manomi zai samu sun hada injin ban ruwa da takin zamani da irin shinkafa da kuma maganin kashe ciyawa na feshi.

Shugaban kungiyar mamonan shinkafa na jihar Taraban yace za a biya bashin ne da zarar an girbe amfanin Gona

Yace ba kamar a baya ba, inda ake rabawa mamonan bashi ba tare da sun ajiye komai ba, yace a wannan karon an bullo da tsarin tabbatar da sai an ga gonar duk wanda za a baiwa bashin tare da gwada girman gonar.

Ya kara da cewa bayan wannan kuma wanda zai amfana da bashin ana bukatar ya bayar da kashi 20 na yawan kudin bashin da za a bashi a matsayin kudin ajiya.

Mallam Tanko Bobbo Andami ya bayyana cewa wanda ya ci gajiyar bashin zai biya sau biyu ne

Ya kuma jaddadawa cewa wannan bashin ba kyauta ba ne, kamar yadda wasu ke zato a baya,watau dole ne duk wanda ya karba ya biya in lokacin biya ya yi.