✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa wadanda ambaliya ta shafa a Nangere

A ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Yobe a karkashin Hukumar Bada Agajin Gaugawa ta Jihar (SEMA), ta aika da kayayyakin tallafi da…

A ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Yobe a karkashin Hukumar Bada Agajin Gaugawa ta Jihar (SEMA), ta aika da kayayyakin tallafi da suka hada kayan abinci da na aikin gida ga al’ummar kauyen Kanda da ke Karamar Hukumar Nangere wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

Kauyen Kanda shi ne kauyen da ambaliyar ruwa ta fi yi wa barna a Jihar Yobe inda kusan duka gidajen da ke kauyen ruwa ya rusa su.

Al’ummar kauyen Kanda sun yaba wa kokarin gwamnatin jihar kan daukar matakin gaggawa, inda ta kai musu gudunmawa don rage musu radadin wannan bala’i da ya same su. Bayan an kididdige barnar da ambaliyar ta yi ne aka kai musu tallafin kasa da awa 24 da faruwar ambaliyar inda suka ce hakan shi ne na farko da gwamnati ta kawo tallafi a kan lokaci a tarihi.

Hukumar SEMA a karkashin jagorancin Shugabanta Dokta Muhammad Mai Goje da kuma Shugaban Karamar Hukumar Nangere Alhaji Baba Langawa da kuma dan majalisar mazabar Nangere a Majalisar Dokokin Jihar Injiniya Saminu Musa Lawan sun je kauyen domin jajanta musu da kuma ba su kayan tallafin.

Shugaban Hukumar  SEMA Dokta Muhammad Mai Goje ya yi kira ga wadanda suka samu tallafin cewa su yi amfani da su yadda ya dace ta hanyar da aka ba su domin amfani da shi ba su sayar ba.

Shugaban Karamar Hukumar ta Nangere da dan majalisar sun gode wa Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni bisa kawo musu kayan agajin da aka yi.

Wadansu magidanta da suka samu tallafin sun gode wa gwamnatin Yobe da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar bisa kawo musu wannan tallafi inda suka yi addu’ar Allah Ya kare sake aukuwar irin wannan bala’i nan gaba.