✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatocin Afirka sun gargadi ’yan kasashensu da ke zaune a Afirka ta Kudu

Bayan barkewar tashe-tashen hankula a wasu biranen Afirka ta Kudu, wadanda suka rutsa da harkokin kasuwancin ’yan kasashen waje, wasu daga cikin kasashen Afirka sun…

Bayan barkewar tashe-tashen hankula a wasu biranen Afirka ta Kudu, wadanda suka rutsa da harkokin kasuwancin ’yan kasashen waje, wasu daga cikin kasashen Afirka sun nuna fargaba tare da jan kunnen ’yan kasarsu da ke zaune a Afirka ta Kudu.

Ofishin Jakandancin Habasha a Afirka ta Kudu ya shawarci ’yan kasar su rufe cibiyoyin kasuwancinsu a lokacin da ake ganiyar tashe-tashen hankulan inda mutanen Afirka ta Kudu ke ta wawaso da cinna wuta a kantunan ’yan kasashen waje a birnin kasuwanci na Johannesburg, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na FBC a Habasha ya ruwaito.

Tun a ranar Litinin ce batagari suka yi ta balle shagunan ’yan kasashen waje tare da kwasar kayayyaki a birnin Johannesburg.

Ofishin Jakadan Habasha ya kuma shawarci ’yan kasar su guji shiga cikin tarzomar kada kuma su kuskura su yi yawo da ababen kawa masu tsada.

Ita ma kasar Zambiya ta bakin Ma’aikatar Sufurinta, ta ce matuka manyan motocin dakon kaya na kasar su daina ratsawa ta cikin kasar Afirka ta Kudu har sai yanayin tsaron kasar ya inganta.

Jawabin da ta fitar na da nasaba ne da rahoton wani harin da aka kai wa matuka manyan motoci ’yan kasar Zambiya tare da yin wasoso da kayan da tirelolin suka yi dakonsu.

Ita kuwa Najeriya ta aike wa jakadan Afirka ta Kudu a kasarta sammaci kan hare-haren kin jinin baki da ake kai wa ’yan Najeriya a kasar.

Ministan Harkokin Kasashen Waje Geoffrey Onyeama ya gana da Jakadan Afirka ta Kudu a ranar Talata kan kashe-kashen na baya-bayan nan da aka fara a karshen makon nan.

Ya kuma ce dole Afirka ta Kudu ta biya ’yan Najeriya diyyar asarar da aka jawo musu.

Onyeama ya wallafa wani sako a Twitter ranar Litinin yana cewa tura ta kai bango, dole Najeriya ta dauki mataki a wannan karo.

’Yan Najeriya da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu tare da yin kira ga gwamnati ta dauki matakin dakatar da kashe-kashen.

Wata kafar labaran Afirka ta Kudu mai suna IOL ta ce, an samu rahotannin cewa an tsare manyan motoci da dama tare da yi musu sace-sace.

Ministan ’Yan sandan Afirka Ta Kudu, Bheki Cele, ya ce “fashi da makami ne ya jawo rikicin ba wai kin jinin baki ba.”

Ya shaida wa manema labarai cewa ana amfani da kalmar kin jinin baki ne kawai don a sakaya zancen. “Babu wani abu da ya jawo tashin hankali tsakanin ’yan kasar da baki,” inji shi.

A wani bangaren kuma, Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda ’yan kasar ke kai hari ga shaguna da wuraren kasuwanci na baki mazauna kasar.

Mista Ramaphosa ya bayyana hakan a wani bidiyon da ya saka a shafinsa na Twitter inda ya ce ’yan kasar ba su da ikon kai hari ga wani bako a tsarin doka.

Ya bukaci shugaban ’yan sandan kasar ya ziyarci wuraren da aka fi samun rikice-rikicen a kasar domin tabbatar da tsaro.