✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni Bakwai na iya komawa APC –Kwankwaso

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce komawa babbar jam’iyyar adawa ta APC yana daya daga cikin zabi hudu da Gwamnoni Bakwai suka…

Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce komawa babbar jam’iyyar adawa ta APC yana daya daga cikin zabi hudu da Gwamnoni Bakwai suka tsara domin ficewa daga Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan.
Gwamna Kwankwaso ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da gidan rediyon bision FM da ke Abuja a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce, sauran zabin sun hada da ci gaba da sulhun da suke yi da Shugaban kasa, ko komawa wata karamar jam’iyya da ba sananniya ba ko kuma kafa sabuwar jam’iyya.
Gwamna Kwankwaso ya nuna takaci kana bin da ya kira rashin katabus na a magance korafe-korafensu daga bangaren shugabannin jam’iyyar da Shugaban kasa duk da cewa takwaransa na Jihar Jigawa yana cikin kungiyar G34 da ta haifi PDP a 1998.
Ya ce, “Duk abubuwan da muka nema daga jam’iyyar da gwamnati da muke ganin su ne mafita ga jam’iyyar ba wanda aka cika. Don haka abin mamamki ne a ga jam’iyya ta kama hanyar yaki da kwamandojinta.”
Kwankwaso ya kuma ce, “Yanzu haka muna da zabi hudu na fita daga wannan rikici idan suka gaza share mana hawaye. daya daga ciki shi ne tattaunawa wanda ake cikin yi, ko shiga waa karamar jam’iyya, kuma wasu sun kawo shawarar kafa sabuwar jam’iyya, sannan wasu suna ganin mu koma Jam’iyyar APC. Ba mu son barin jam’iyyar. Amma idan barin PDP shi ne kawai zai cici jihohinmu da jama’armu, za mu bar ta. A kan haka muna kira ga jama’a su ba mu goyon baya, domin damuwarmu ita ce kawar da duk wani abin da zai cutar da jama’armu.”
Game da hakikanin takaddamarsu da PDP bangaren Bamanga, Kwankwaso ya ce, “Muna son su warware rikicin Jihar Ribas inda aka rusa shugabannin PDP. Amaechi ya ci zaben Majalisar Gwamnoni da kuri’a 18, ina wurin. Amma wani mai kuri’a 16 yana da’awar shi ya ci zaben. Sannan a Adamawa, mun ce a magance matsalar can da sauran batutuwa da muka ce akwai bukatar a magance su.”
Gwamnan na Kano ya sake nanata fatalinsa da taron kasa da ake shirin yi, inda ya ce mutanen da suke goyon bayansa su ne, wadanda “suke son zuwa su kwanta a otel-otel masu tsada a Abuja sannan su karbi kudi daga hannun gwamnati lokacin da aka kammala taron.”
“Ba na goyon wannan taro. Na fadi haka a ranar da Shugaban kasa ya sanar da shi. Za bata dukiya da lokaci ne kawai, a karshe yana iya jawo wata matsalar da wadanda suka kawo shawarar ba su san za ta zo ba. Ni a kashin kaina ba na goyon bayansa. To amma siyasa ake yi, don haka za mu kira taron dattawa a Kano. Lokacin da nake Ministan Tsaro an yi irin wannan taro kuma an kashe kudi mai yawa. Amma da za ka tambaye ni a yanzu ina rahoton wancan taro a yanzu ban san inda yake ba,” inji shi. Ya shawarci gwamnati ta karkatar da kudin da za ta kashe kan taron zuwa kan ayyukan raya kasa a sassan kasar nan.