Da Dumi Dumi

Gwamnoni shida sun yi taron sasanci da Shugaban kasa

Gwamnoni shida a karkashin jagorancin Gwamna Rotimi Amaechi na Jihar Ribas, wanda kuma shi ne shugaban majalisar gwamnoni ta Najeriya, sun yi wani taro da Shugaban Goodluck Jonathan a gidan gwamnati a Abuja a ranar Litinin da dare.
Gwamnonin su ne Mu’azu Babangida Aliyu na Jihar Neja da Rabi’u Musa Kwankwaso na Jihar Kano da Sule Lamido na Jihar Jigawa da Murtala Nyako na Jihar Adamawa da Abdulfatah Ahmed na Jihar Kwara. Ba a bayyana wata ajanda ta taron ba, amma ana kyautata zaton an motsar da shi ne don a samar da hanyoyin sasantawa da Shugaba Goodluch Jonathan.
Gwamna Rotimi Amaechi shi ne yake shugabantar bangare daya na majalisar gwamnoni ta Najeriya, wanda shugaban kasa bai yi na’am da shi ba.
Gwamnoni hudu daga cikin wadanda suka hallara sun yi ta zagayawa a cikin kasa suna saduwa da wadansu dattijai suna neman su taimaka wajen kawo karshen tashin-tashinar da ake ta samu a cikin kasa dangane da inda siyasa ta fuskanta.

Share