✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni za su gana da Malami kan ‘yancin bangaren shari’a da na majalisa

Gwamnoni za su tattauna da Gwamantin Tarayya kan sabuwar dokar da Shugaba Buhara ya rattaba wa hannu kan ‘yancin cin gashin kai ga matakan gwamnati…

Gwamnoni za su tattauna da Gwamantin Tarayya kan sabuwar dokar da Shugaba Buhara ya rattaba wa hannu kan ‘yancin cin gashin kai ga matakan gwamnati daban-daban.

Gwamnonin jihohi 36 sun amince su tattauna da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati, inda suka wakilata kwamitinsu shari ‘a na kungiyarsu domin tattaunawa da mininstan.

Kwamitin ya kunshi gwaman Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, Simon Lalong na Filato da kuma Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Hakan na kunshe ne a takardar bayan taron bidiyo karo na tara da shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya fitar.

Abin da sabuwar dokar ta kunsa

A ranar Jumu’ar da ta gabata ne dai shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar ba wa bangaren shari’a da majalisun jihohi ‘yancin cin kashe kudadensu.

Hadimin ministan shari’a kan harkar yada labarai, Dr Umar Gwandu ya fitar, ya ce ya dokar ta dace da da damar da sassa na biyar da kuma na 121 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya su ka ba Shugaban.

Aikin kwamitin gwamnoni

Gwamnonin dai sun dora wa kwamitin alhakin tabbatar da aiwatar da dokar kamar yadda sashe na 121 (3) na kundin tsarin mulki da aka yi wa kwaskwarima ya tsara.

Fayemi ya kuma ce ya yi wa gwamnoni bayani inda tattaunata ta kwana tsakaninsu da kwamitin kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar da kuma gidauniyar masu zaman kansu da ke taimakawa kasar wajen kawo karshenta a Najeriya.

Masu ba da tallafin yaki da coronavirus

Hakazalika, gwamnonin sun saurari bayanai daga babban jami’in Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) a nan Najeriya, Ebrima Faal, kan batun tallafin Dala biliyan daya da kasar za ta ci gajiya.

Sun gana da Zouera Youssoufou, manajan darakta kuma shugaban Gidauniyar Dangote (Dangote Foundation) a madadin gamayyar masu zaman kansu da ke taimakawa wajen yaki da annobar ta corona.

Tallafin bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB)

Gwamnonin sun amince su shiga tsakani a tattaunawar da ma’aikatar kudi ke yi da Banki Raya Kasashen Afirka kan Dala biliyan daya da Najeriya za ta amfana don gudanar da wasu ayyuka a bangarorin lafiya, harkokin noma da kuma samar da abinci.

Rabon kayan tallafin coronavirus

Sun kuma amince su ci gaba da shirin rarraba kayan rage radadin da kullen annobar coronavirus ya tilasta, musamman ga masu tsananin bukata.

Shirin bude harkokin kasuwanci

Fayemi ya kuma ce gwamnonin sun amince da tsara yadda za a sake bude harkokin kasuwanci a cikin watanni uku.

Za a yi tsarin ne tare da kwamiti da majalisar zartarwa ta kasa ta kafa da kuma kwamitin kar-ta-kwana na yaki da cutar coronavirus.

Kwamitinin ya kunshi gwamnonin jihohin Delta da Legas da Ekiti da Kano da Anambra da Bauchi da Filato da kuma ministan Babban Birnin Tarayya Abuja.