✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin APC sun taya Buhari murnar cika shekara 77

Kungiyar Gwamnonin APC ta taya Shugaba Kasa Muhammadu Buhari murnar cika shekara 77 a duniya. A ranar Talata ce Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Kebbi…

Kungiyar Gwamnonin APC ta taya Shugaba Kasa Muhammadu Buhari murnar cika shekara 77 a duniya. A ranar Talata ce Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudu, ya aike da sakon a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu. Ya ce kungiyar tana alfahari da kasancewa tare da Shugaba Buhari wanda ta kira ‘Shugaba abin koyi’ ga dukkan al’ummar wannan zamani.

Gwamna Bagudu ya yi wa Shugaba Buhari godiya kan jajaircewarsa wajen ganin Najeriya ta kai bantenta.

Ya ce “Kungiyar Gwamnonin APC na taya Shugaban Kasa Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa tare kuma da gode masa kan gudunmawar da yake bayarwa ga kasarmu. Muna matukar alfahari da irin jarumtarsa da adalcinsa wajen tafiyar da mulkin kasar nan. Ka kasance Shugaba abin koyi ga jama’ar wannan zamani kuma muna yi maka fatar alheri.”