✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin APC sun yi ganawar sirri da tsohon Shugaba Jonathan

Ba a bayyana abin da aka tattauna ba, amma wata majiya ta ambato 2023

Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC sun yi wata ganawar sirri da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a gidansa da ke Abuja.

Gwamnan Jihar Yobe, kuma Shugaban Kwamitin Rikon Kwarya na jam’iyyar ta APC, Mai Mala Buni, shi ya jagoranci gwamnonin da suka halarci taron.

Duk da dai ba a bayyana abin da suka tattauna a zaman ba, wata majiya mai kusanci da taron ta ce yana da nasaba da “shirye-shiryen zaben 2023”.

Sai dai kuma an ce babu wani gwamnan jam’iyyar PDP da ya halarci zaman na ranar Juma’a.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamnan Ebonyi, David Umahi, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, da Atiku Bagudu na Kebbi, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, da kuma Abubakar Badaru na Jigawa.

Akwai kuma Kashim Ibrahim-Imam, tsohon wakilin Shugaban Kasa a kan harkokin da suka shafi Majalisar Dokoki ta Kasa.

Tsawon lokaci

An ce gwamnonin sun kwashe tsawon lokaci suna tattaunawa da tsohon shugaban kasar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnonin suke kai wa Jonathan ziyara ba.

Ko a bara Gwamna Abubakar Badaru da Gwamna Atiku Bagudu sun ziyarce shi a gidansa da ke Otuoke, Jihar Bayelsa.

Gwamnonin sun kai masa ziyarar ne domin yin godiya da taimakon da ya bai wa dan takarar gwamnan jam’iyyarsu, David Lyon, wanda ya lashe zabe a shekarar 2019.

Daga bisani dai Kotun Koli ta soke zaben ta kuma dora dan takarar PDP, Douye Diri, a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kotun ta soke kuri’un David Lyon ne saboda samun mataimakinsa da laifin amfani da takardun shaidar karatu na bogi.

Murnar shekara 63

A ranar Juma’ar dai, shugabannin APC, ciki har da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ken Nnamani, suka kai wa Mista Jonathan ziyarar murnar cikarsa shekara 63.

Ita ma Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya wadda Gwamnan Filato Simon Lalong ke jagoranta, ta tura wa Shugaba Jonathan sakon murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

A sakon nata, kungiyar ta ce har yanzu Goodluck Jonathan mutum ne mai kwazo wajen yi wa kasa aiki.

Sun ce shi dan siyasa ne nagari wanda ke tsananin son cigaban demokradiyya, abin da ya fito karara a lokacin da yake mulki da kuma tafiye-tafiyen da yake yi a yanzu na sa ido a zabubbukan da ake gudanarwa a fadin duniya.

Sanin kowa ne cewar har yanzu Jonathan yana da sauran damar shugabantar Najeriya na wa’adi daya mai shekara hudu.

Ya yi wa’adin mulki daya bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekarar 2011.

Sai dai a yunkurinsa na yin tazarce a 2015 ya sha kaye a wruin dan takarar APC, Muhammadu Buhari.