✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin APC sun yi taro kan rashin aikin yi a kasar nan

kungiyar Gwamnoni Masu Ra’ayin Sauyi (PGF) ta Jam’iyyar APC ta gudanar da taro a Ibadan a ranar Litinin inda ta koka kan matsalar rashin aiki…

kungiyar Gwamnoni Masu Ra’ayin Sauyi (PGF) ta Jam’iyyar APC ta gudanar da taro a Ibadan a ranar Litinin inda ta koka kan matsalar rashin aiki da rikicin shugabanci da ya dabaibaye mahukumta.
Gwamnonin sun bayyana cewa, damuwarsu a kan halin kunci da miliyoyin jama’a ke ciki, ita ce ta bambanta jam’iyyarsu APC da Jam’iyyar PDP mai mulki wadda ta yi biris da irin wadannan matsaloli da Najeriya ta samu kanta a ciki.
Shugaban kungiyar Gwamnoni Masu Ra’ayin Sauyi kuma Gwamnan Jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha, ya ce, kungiyar ta shirya taron na Ibadan mai taken “Matsalar Rashin Aiki da Rikicin Shugabanci a Najeriya: Ina Mafita?” a karon farko, kuma za a yi irin wannan taro karo na biyu a Jihar Kano domin tattaunawa a kan matsalar ilimi, sai karo na uku da za a yi a Jihar Imo a kan matsalar kiwon lafiya, yayin da a Jihar Kwara da za ta shirya taro karo na hudu kuma na karshe a bana za a gabatar da kasidu a kan matsalar albarkatun ruwa.
 “Wannan, alamomi ne da ke nuna irin damuwarmu da irin gurguncewar al’amura a kasar nan da muke fafutikar samo mafita,” inji shi.
 Kafin fara taron sai da Shugaban Jami’yyar APC, Cif Bisi Akande da tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da tsohon Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Bello Masari suka jagoranci tawagar gwamnonin zuwa filin wasa na Lekan Salami domin yi wa dimbin magoya bayansu jawabai.
A zauren taron na Cibic Centre, gwamnonin jihohin Oyo, Abiola Ajimobi da na Ekiti, Kayode Fayemi da na Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso sun yi jawabai ne dangane da muhimmancin kawo sauyi a cikin al’amuran da suka shafi rayuwar talakawa musamman rashin aikin yi da miliyoyin jama’a ke fuskanta da matsalar rikicin siyasa.
Gwamnonin jihohin Ogun da Sakkwato da Adamawa da Ekiti da Kano da Imo da Oyo Ribas ne suka halarci taron na Ibadan, a yayin da sauran gwamnonin na APC suka aika da mataimakansu.