✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin Arewa maso Yamma na taro akan tsaro a Katsina 

Yanzu haka ana gudanar da taron Gwamnonin Jihohin Arewa maso Yamma a gidan Gwamnati na Jihar Katsina. Taron dai ci gaba ne akan tarurrukan da…

Yanzu haka ana gudanar da taron Gwamnonin Jihohin Arewa maso Yamma a gidan Gwamnati na Jihar Katsina. Taron dai ci gaba ne akan tarurrukan da ake yi don bullo da hanyoyin magance matsalar tsaro da ta shafi wadannan jihohi.

Wadanda suka halarci taron na yau sun hada da: Gwamnonin jihohin Kano, Kebbi, Sokoto, Neja, Kaduna da kuma Jahar Katsina mai masaukin baki tare da Kwamandan Birget ta 17 da ke Jahar Katsina Babban Sufeton Ƴansanda na Kasa. Saura mahalarta taron sun hada da kungiyoyin sa kai da na Miyetti Allah da sauran masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro.

Taron na da nufin samar da hanyoyin sasanci kamar wanda ake cikin yi a halin yanzu a Zamfara wanda da ma can a Jahar Katsina ne aka fara yinsa domin tsayar da zubar da jinin da ake cikin yi a wadannan jihohin.