✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin Arewa sun ba iyalan jami’an tsaro da ’yan Ombatse suka kashe Naira miliyan 100

kungiyar Gwamnonin Arewa ta ba iyalan jami’an tsaro sama da 100 da ’yan kungiyar matsafan kabilar Eggon a Jihar Nasarawa da aka fi sani da…

 Gwamna Babangida Aliyukungiyar Gwamnonin Arewa ta ba iyalan jami’an tsaro sama da 100 da ’yan kungiyar matsafan kabilar Eggon a Jihar Nasarawa da aka fi sani da Ombatse suka kashe a kauyen Alakyo da ke karamar Hukumar Lafiya kwanakin baya.
Da yake mika kudin ga Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura a gidan gwamnati da ke Lafiya, shugaban kungiyar gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Neja Alhaji Babangida Mu’azu Aliyu ya yaba wa Gwamna Umaru Al-Makura game da kafa kwamitin binciken kisan gillar da aka yi wa jami’an tsaron.
Gwamna Babangida Aliyu ya ce babban dalilin ziyararsu zuwa jihar shi ne su jajanta wa Gwamnan da al’ummar jihar dangane da wannan mummunan al’amari kuma su karfafa wa Gwamnan domin ba shi damar ci gaba da gudanar da kyakkyawan shugabancin da yake yi a jihar.
Ya yaba wa Gwamnan kan haramta kungiyoyin asiri a jihar ya ce babu shakka hakan wani mataki ne da zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da jihar ta tsinci kanta a ciki.
Da yake maida jawabi Gwamna Al-Makura ya mika godiya a madadin gwamnatin jihar da iyalan jami’an tsaron ga kungiyar Gwamnonin Arewa kan wannan karamci da ziyarar da suka kai jihar. Gwamna Al-Makura ya ce za a yi amfani da kudin yadda ya dace. Ya ce “Jihar Nasarawa kamar jiha ce mai albarka da ake zaune lafiya. Amma abin bakin ciki shi ne yadda wasu batagari da ba sa son ci gabanta suka fara bata sunanta.”
A cikin tawagar gwamnonin da suka rufa wa Gwamna Babangida Aliyu baya akwai Gwamna Sule Lamido na Jihar Jigawa da Alhaji Mukhtar Ramalan Yero na Jihar Kaduna da Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Abdullahi Faskari da tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu da sauransu.