✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin da suka haye siradi a Kotun Koli sun yi kira a hada hannu wuri daya

Hukunce-hukuncen da Kotun Koli ta yanke kan kararrakin zaben gwamnonin jihohi da aka gabatar a gabanta sun kawo karshen tataburzar siyasa da ta dabaibaye jihohin…

Hukunce-hukuncen da Kotun Koli ta yanke kan kararrakin zaben gwamnonin jihohi da aka gabatar a gabanta sun kawo karshen tataburzar siyasa da ta dabaibaye jihohin Kano da Sakkwato da Bauchi da Filato da Benuwai da Adamawa, bayan da kotun ta kammala yanke hukunci kan shari’un da suka shafi jihohin.

Tuni gwamnonin jihohin wadanda kotun ta tabbatar musu da nasararsu a zaben bara suka bayyana farin cikinsu kan nasarar da suka samu a kotun, inda wadansu suka nuna farin ciki tare da kira ga abokan adawa su zo a hada hannu domin ciyar da jihohin nasu gaba.

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya yaba wa magoya bayansa kan hakurin da suka yi na ba kotu damar tabbatar da adalci. Sannan ya yi alkawarin cire wa al’ummar jama’ar kitse a wuta. Ya fadi haka ne a hira da manema labarai a ranar Litinin bayan Kotun Kolin ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya samu nasara a zaben Gwamnan Jihar da ya gabata.

Barista Mohammed Abdullahi Abubakar na Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar ne ya kalubalanci nasarar Gwamna Bala Mohammed yana zargin an tafka magudi a zaben. Sai dai dukkan alkalan kotun biyar sun yi watsi da karar, tare da tabbatar da zaben Sanata Bala Mohammed.

Da yake hira da gidan rediyon BBC jim kadan da kammala shari’ar, Gwamna Bala Mohammed ya ce wannan nasara ce ta al’ummar Jihar Bauchi ba tasa shi kadai ba. “Zan tabbatar da cewa na cika wa mutanen Bauchi muradinsu, zan cire musu kitse daga wuta’,’ inji Gwamnan.

Kan zaben Gwamnan Jihar Filato ma Kotun Kolin ta tabbatar da zaben da aka yi wa Gwamna Simon Bako Lalong na Jam’iyyar APC .

Dan takarar Jam’iyyar PDP, Sanata Jeremiah Useni ne ya shigar da kara yana zargin cewa an yi magudi a zaben, sai dai hujjojin da ya gabatar ga kotun sun gaza gamsar da ita a kan ikirarin nasa.

A hirarsa da BBC jim kadan da tabbatar da nasararsa, Gwamna Lalong ya nemi abokan hamayyarsa, su zo a hada hannu a yi tafiya tare domin ciyar da jihar gaba.

Gwamnan Jihar Kano da Kotun Kolin ta  tabbbar Dokta Abdullahi Ganduje, ya ce ya yafe wa kowa kuma yana neman abokan adawa su zo a hada hannu don ciyar da Jihar Kano gaba.

A ranar Litinin ce kotun ta yanke hukunci kan shari’o’in da ke gabanta ciki har da ta Kano inda Kotun Kolin ta yi watsi da karar dan takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da tabbatar wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kujerar.

Bayan haka kotun ta yi watsi da karar da Alhaji Ahmed Aliyu na Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato ya shigar gabanta, inda kotun ta tabbatar da Alhaji Aminu Waziri Tambuwal na PDP a matsayin Gwamnan Jihar.

Hakazalika kotun ta tabbatar da zaben Gwamnan Jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri inda ta yi watsi da karar da Alhaji Muhammad Jibirila Bindow ya shigar gabanta. Haka kotun ta tabbatar da zaben Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai a karkashin Jam’iyyar PDP, bayan ta kori karar Mista Emmanuel Jeme na APC bisa rashin hujja.

Sai dai a makon jiya ne kotun ta kori Gwamnan Jihar Imo, Mista Emeka Ihedioha na Jam’iyyar PDP daga kujerarsa inda ta bai wa Sanata Hope Uzodinma na Jam’iyyar APC kujerar, bayan da ta sa aka dawo da wasu kuri’unsa da Hukumar INEC ta cire lokacin zabe ba tare da dalili ba.