✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Gwamnonin G7 sun ziyarci Obasanjo

A daidai lokacin da rikicin cikin gida na Jam’iyyar PDP ke dada daukar sabon salo gwamnonin nan bakwai da ake kira G-7 sun ziyarci tsohon…

A daidai lokacin da rikicin cikin gida na Jam’iyyar PDP ke dada daukar sabon salo gwamnonin nan bakwai da ake kira G-7 sun ziyarci tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Litinin da ta gabata a gidansa da ke Hilltop a garin Abeokuta hedkwatar Jihar Ogun, inda suka yi wata ganawar sirri da shi.

Bayan ganawar ta tsawon awa 2, Gwamnan Jihar Neja Mu’azu Babangida Aliyu, ya shaida wa ’yan jarida cewa, suna ziyartar dattijan Jam’iyyar PDP ne domin nema su tsoma bakinsu a samo hanyar sasanta tsakaninsu da Shugaba Goodluck Jonthan, kuma suna sa ran tsohon Shugaban zai taka rawa wajen shawo kan takaddamar da ta ki ci ta ki cinyewa.
Gwamna Babangida Aliyu, ya ce, “Tun daga lokacin da matsalar ta kunno kai muke ziyartar dattijan jam’iyyar domin ganawa da su. Kuma a matsayin sa na tsohon shugaban kasa ko tsohon shugaban kwamitin amintattu na PDP, mun zo ne domin yin irin wannan ganawa da shi, inda muke sa ran nan da kankanen lokaci za a sasanta.” Dangane da yiwuwar komawarsu Jam’iyyar APC, Gwamna Aliyu, ya ce, “Ba ni da masaniya dangane da hakan jita jita ce kawai ake yadawa.”
Gwamnoni 5 da suka kai ziyarar sun hada da Mu’azu Babangida Aliyu da Rabi’u Musa Kwankwaso na Kano da Murtala Nyako na Adamawa da Rotimi Amaechi na Ribas da Sule Lamido na Jigawa, yayin da Aliyu Magatakarda Wammako na Sakkwato da Abdulfatah Ahmed na Kwara, ba su samu zuwa ba.