✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin ku farfado da ayyukan malaman gona a jihohinku – Masana

Daraktan Kungiyar Shirya Ayyukan Manoma ta ‘Sasakawa 2000’ a Najeriya Farfesa Sani Miko ya koka kan yadda gwamnonin jihohi suka yi wa sashin malaman gona…

Daraktan Kungiyar Shirya Ayyukan Manoma ta ‘Sasakawa 2000’ a Najeriya Farfesa Sani Miko ya koka kan yadda gwamnonin jihohi suka yi wa sashin malaman gona rikon sakainar kashi tare da nuna halin ko-in-kula da su.

Farfesa Miko ya bayyana haka ne a wajen taron shekara-shekara na Sasakawa a dakin taro na Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello (NAERLS) da ke Zariya, inda aka yi bitar kan ayyukan da suka gudanar tare da shawarar yadda za su inganta aikace-aikacensu a bana. Ya ce, babban abin takaici shi ne yadda a wasu jihohi babu malaman gona  da za su wayar da kan manoma duk da dimbin manoman da Allah Ya albarkace su da su, a yayin da a wasu jihohin za ka iske malamin gona daya ne yake kula da manoma dubu uku.

A cewarsa, wannan dabi’ar ba zai haifar wa Najeriya da mai ido ba, kuma ya zama wajibi ga gwamnonin jihohin su sake tunani don farfado da ayyukan malaman gona a jihohinsu.

Farfesa Sani Miko ya ce, a bana jihohi 6 sun samu shiga cikin shirye -shiryensu, jihohin su ne: Kogi, da Bauchi da Jigawa da Ribas da Ondo, da kuma Abiya. Ya ce, a wannan karon sun samu wani canji mai amfani inda kwararrun masana da suka shahara wajen yada aikace- aikacen da Sassakawa SG2000 ke yi ta hannun malaman gona wanda ya ba manoman damar cin gajiyar shirin inda suka horar da malaman gona a fannin dabarun aikin gona.

Daraktan ya bayyana taron na bana a matsayin wanda zai magance  matsalolin da ake cin karo da su tare da samar da yadda za a ci gaba a kan matsalolin da suka faru.

Shi ma da yake jawabi Babban Sakataren Ma’aikatar Gona da Raya Karkara, Dokta Mohammed Bello Umar, ya ce matsakaitan manoma su ne abin bai wa muhimmanci matukar ana son cimma burin samar da wadataccen abinci a kasa.

Dokta Bello Umar ya bayyana gamsuwa bisa yadda ma’aikatarsu ke tafiya kafada-da-kafada da malaman gona domin a samar do nasarar da ake bukata na ciyar da kasa ba tare da an shiga wani yanayi marar dadi ba.