✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin Najeriya da suka kamu da coronavirus

Tun bayan bullar annobar  Coronavirus a Najeriya aka tabbatar da wasu gwamnoni shida sun kamu da cutar. A ranar Juma’a 28 ga watan Fabrairu 2020…

Tun bayan bullar annobar  Coronavirus a Najeriya aka tabbatar da wasu gwamnoni shida sun kamu da cutar.

A ranar Juma’a 28 ga watan Fabrairu 2020 ma’aikatar lafkiya ta sanar da mutum na farko da ya harbu da cutar a jihar Legas wanda yake dan kasar Italiya ne kuma shi ne ya shigo da  cutar cikin Najeriya a ranagr 25 ga Fabrairu 2020.

Najeriya dai ta kasance kasa ta uku a Nahiyar Afirka da ke adadin masu cutar bayan kasashen Aljeriya da Egypt. Adadin na ci gaba da karuwa duk da matakin da hukumomin gwamnati ke  dauka na hana yaduwar cutar.

A yanzu haka dai an shiga wnata na hudu ke nan bayan bullar annobar a kasar inda ake da adadin sama da mutum dubu 25 da suka kamu.

Gwamnoni shida da suka kamu

Gwamnan jihar Bauchi

A ranar 24 ga watan Maris ne sakamakon wani gwaji da aka yi ya nuna cewa Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammmed, yana dauke da cutar Coronavirus.

A wata sanarwa da babban mai bai wa gwamnan shawara a kan kafofin yada labarai Mukhtar Gidado ta tabbatar da hakan. Inda ya ce bayan gwajin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta yi an tabbatar da mutum shida ne suka kamu da cutar.

Daga bisani aka shiga zaman zullumi a Bauchi bayan da gwamnan jihar, Bala Mohammed, da kwamishinoninsa guda biyu suka killace kansu sakamakon mu’amala da dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda aka tabbatar yana dauke da cutar Coronavirus.

Gwamnan jihar Kaduna

A ranar 28 ga watan Maris gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya bi sahun mutanen da ta tabbata sun kamu da cutar Coronavirus.

Gwamnan ne ya bayyana hakan da bakinsa a wani hoton bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Gwamnan ya kuma ce kamar yadda ka’idojin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) suka tanada tuni ya killace kansa.

A ranar 22 ga Afrilu Gwamnan ya sanar da cewa ya warke daga cutar bayan wasu makonni yana killace.

Gwamnan jihar Oyo

A ranar 30 ga watan Maris 2020, Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, ya bayyana cewa gwajin da aka yi masa na cutar Coronavirus ya nuna cewa yana dauke da cutar.

Seyi Makinde, ya shaida hakan ne a shafinsa na Twitter @seyiamakinde, da yammacin ranar  Litinin 30 ga watan Maris, inda ya bai wa tsohon babban Daraktan sashin lafiya na Asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan Farfesa Temitope Alonge, jan ragamar tawagar da ke kula da yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

Bayan kwanakin shida yana killace a ranar 6 ga watan Afrilu ya sanar da cewa ya warke  daga cutar.

Gwamnan jihar Abia

A ranar 8 ga watan Yuni aka sanar da cewa, an killace Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia bayan ya harbu da cutar coronavirus.

Ikpeazu ya killace kansa ne tun bayan fitowar sakamakon gwajin da ya tabbatar da ya kamu da cutar coronavirus, a cewar Kwamishinan Yada Labaran jihar John Okiyi Kalu.

Gwamnan jihar Ondo

A ranar Talata 30 ga watan Yuni, 2020 aka sanar da cewa Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo ya kamu da cutar COVID-19.

Gwamna Akeredolu a cikin wani bidiyo, ya ce sakamakon gwajin cutar da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar COVID-19, kuma zai fara killace kansa, domin likitoci su kula da lafiyarsa.

Gwamnan jihar Delta

 

A ranar Laraba 1 ga watan Yuli aka sanar da cewa, Gwamnan jihar Delta, Dakta Ifeanyi Arthur Okowa tare da maidakinsa sun kamu da COVID-19.

Gwamnan ya sanar da hakan na a shafinsa na twitter, @IAOkowa.

“Da ni da maidakina gwajin da aka yi mana ya nuna sakamakon cewa, muna dauke da cutar COVID-19. Muna cikin koshin lafiya za mu ci gaba da killace kanmu. Mun gode da addu’o’in jama’a da ’yar mu.” Inji Gwamnan.

A ranar Juma’ar makon da ya gabata ne sakataren watsa labarai na gwamnan Mista Olisa Ifeajika ya sanar da cewa ’yar gwamnan Delta ta kamu da cutar COVID-19.