✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin PDP 5 sun koma APC

Gwamnoni biyar daga cikin gwamnonin G7 na Jam’iyyar PDP sun koma sabuwar Jam’iyyar APC, sakamakon hadewar bangarorin biyu lamarin da ya kawo babban kalubale ga…

Daga dama Alhaji Kawu Baraje, sai Mista Tempre Sylva  da Cif Ogbunna Onu da Cif Bola Tinubu da Sanatta Abdullahi Adamu da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, lokacin bayyana hadewar sabuwar PDP da Jam’iyyar APC a ranar Talata a Abuja.Gwamnoni biyar daga cikin gwamnonin G7 na Jam’iyyar PDP sun koma sabuwar Jam’iyyar APC, sakamakon hadewar bangarorin biyu lamarin da ya kawo babban kalubale ga jam’iyya mai mulki.
Ficewar gwamnonin da suka hada da Rotimi Amaechi (Ribas) da Rabi’u Kwankwaso (Kano) da Murtala Nyako (Adamawa) da Aliyu Wamakko (Sakkwato) da kuma Abdulfatah Ahmed (Kwara), yawan gwamnonin PDP ya dawo 18.
Sai dai gwamnonin Jigawa Sule Lamido da takwaransa na Neja Mu’azu Babangida Aliyu – sun ki bin Gwamnonin G-7 din inda suka zabi ci gaba da zama a Jam’iyyar PDP.
Da misalign karfe 11:46 na safe ne aka bayyana hadewarsu da APC a wata takardar bayan taro da Shugaban Sabuwar PDP Alhaji Abubakar Baraje, ya karanta wa manema labarai, bayan doguwar tattaunawa a masaukin baki na Gwamnan Kano da ke Abuja.
“Wani taron shugabannin Jam’iyyar APC da na sabuwar PDP da suka hadu a safiyar yau, (Talata) a gidan Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso a Abuja, bayan doguwar tattaunawa jam’iyyun biyu sun amince su hade domin ceto dimokuradiyyar kasar nan daga halaka,” inji takardar bayan taron. Baraje da shugaban riko na Jam’iyyar APC Cif Bisi Akande suka sanya hannu kan takardar.
Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnonin Ribas da Kano da Kwara da Adamawa da Neja, sai dai ana cikin taron Gwamnan Neja ya tafi, a abin da ake ganin alamar rashin amincewa da hadewa da APC. Shi kuma Gwamnan Jigawa bai halarci taron ba, yayin da takwaransa na Sakkwato Wamakko aka ce an wakilce shi a wurin taron saboda ya fita kasar waje.
Daga baya Kwankwaso ya shaida wa sashin Hausa na BBC Landan cewa su da suke cikin sabuwar PDP sakamakon wannan hadewa za su tuntubi magoya bayansu don yanke shawara kan inda za su nufa.
Lokacin da aka tuntubi kakakin Wamakko, Sanu Umar ya ce Gwamnan yana kasar waje, ba zai iya samunsa ba domin tabbatar da ko ya koma APC. Amma kakakin Gwamnan Jihar Kwara Malam Mu’iddeen Akorede ya ce, Gwamna Ahmed ya koma APC.
Sauran shugabannin da suka halarci taron sun hada da Sakataren Sabuwar PDP Olagunsoye Oyinlola, da Mataimakin Shugabanta na kasa Sam Jaja da tsohon Gwamnan Bayelsa Timipre Sylba da Sanata Abdullahi Adamu da kuma Sanata Bukola Saraki.
Aminiya ta samu bayanin cewa yanke shawarar hadewa da APC an yi ne domin karya shirin PDP na korar shugabannin sabuwar PDP daga uwar jam’iyyar.
Jam’iyyar PDP a karkashin Bamanga Tukur ta dakatar da hudu daga cikin shugabannin bangaren da suka hada da—Baraje da Oyinlola da Jaja da kuma shugabanta na shiyyar Arewa maso Yamma Ibrahim Kazaure.
An kuma bukaci su hallara a gaban kwamitin ladabtarwa a ranar Talatar da ta gabata, inda suka ce ba za su halarta ba.
Aminiya ta samu labarin cewa shugabannin sabuwar PDP da Gwamnonin G-7 sun yanke shawarar dauka mataki mai zafi kafin Jam’iyyar PDP ta wulakanta su. Kuma saboda haka ne suka kira taron inda mafi yawan gwamnonin da suka halarta suka yi ittifakin nuna goyon baya ga shugabannin bangarensu. Sun ce yunkurin korarsu da Jam’iyyar PDP ke yi an yi ne domin a karya lagon bangaren. A wurin taron sun jinjina zabin shiga Jam’iyyar APC ko sabuwar Jam’iyyar PDM ko yin rajistar wata sabuwar jam’iyya.   
Shugabannin Jam’iyyar APC da suka hada da Sanata Bola Ahmed Tinubu da Ogbonnaya Onu da Bisi Akande, daga baya sun isa wurin taron, inda aka daddale batun hadewar.
Wata majiya a wurin taron ta ce, da farko an duba yiwuwar hadin gwiwa, yayin da wasu gwamnonin G-7 suka nace cewa ana ci gaba da tattaunawa fa Shugaba Jonathan, amma mafi yawa suka nace cewa jan kafa zai iya sa su rasa madafa.
Da yake bayani a wurin bayyana hadewar Tinubu ya ce suna daukar mataki a lokacin domin tabbatar nasarar hadewar.
 “Ba za mu yi dogon bayani kan dabarunmu ga manema labarai gaba daya ba; yana da kyau mu dan gutsura muku kadan domin kada ko jawo rudu a ko’ina. Muna farin ciki da ci gaban da aka samu, mun dauki alkawarin ceto kasarmu daga rugujewa, kuma muna tsaye a kungiyance domin karfafa bukatun kasar nan,” inji shi.

Muna nan a PDP – Gwamna Lamido da Aliyu
Da yammacin ranar kuma sai kakakin Gwamna Sule Lamido Malam Umar Kyari Jitau ya fitar da wata sanarwa cewa “Yayin da na yarda cewa jam’iyyarmu ta PDP tana cikin matsala da rikita-rikita sakamakon rashin iya jagorancin Shugaban Jam’iyyar PDP Bamanga Tukur, wannan ba zai sa na wargaza tarihin siyasata ba, a ce wai na koma wata jam’iyya ba.”
Gwamna Lamido ya ce,” Gaskiya ce muna fuskantar musgunawa ni da iyalaina muna cikin wani
kuncin siyasa, lamarin da ya sa ake kokarin cin zarafina da na iyalina, hakan ba zai sa na bar jam’iyyar ba. Babu wata barazana da za ta sa na fice daga Jam’iyyata ta PDP ba, ba zan ba wani wannan damar ba, da za a ce na koma wata jam’iyyar da wani zai samu damar juya ni ballantana a ce ya mallake ni.”
Gwamna Lamido ya ce “Ina nan daram a cikin jam’iyyarmu ta PDP babu gudu babu ja da baya domin ni uba ne a cikin PDP mu ne muka kafa ta.”
A nasa bangaren Gwamnan Jihar Neja ta bakin kakakinsa danladi Ndayebo, ya ce ya kadu lokacin da ya ji sanarwar hadewar sabuwar PDP da APC, tun kafin a yanke shawara ta karshe kan batun. Ya ce ana ci gaba da tattaunawa da Shugaba Jonathan, kuma za su jira sakamakon tattaunawar kafin yanke shawara a kai.

Ba mu damu ba
– PDP
Jam’iyyar PDP ta mayar da martani kan komawar gwamnonin Jam’iyyar APC, inda ta ce ba ta damu ba.
Kakakin Jam’iyyar na kasa Olisa Metuh ya ce, “Muna fada da babbar murya cewa PDP ba ta damu ba, domin yanzu mun yawa kwallon mangwaro mun huta da kuad. Muna kira ga ’ya’yan jam’iyyarmu a fadin kasa su hada kai a wannan lokaci da masu son wargazata suka bar cikinmu.”
Metuh ya kara da cewa, “Muna tunatar da mambobinmu cewa daga hukunci da kotu ta yanke babu wani bangare a PDP. A idon shari’a PDP daya ce kanta a hade a karkashin shugabancin Alhaji Bamanga Tukur.”