✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamntin Kaduna za ta haramta wa likitocin gwamnati aiki a asibiticoci masu zaman kansu

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatinsa za ta samar da wata doka da za ta haramta wa…

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatinsa za ta samar da wata doka da za ta haramta wa likitoci da ke aiki a asibitocin Gwamnatin Jihar bude wa ko yin aiki a asibitoci masu zaman kansu a jihar.

Gwamnan ya ce duk wanda ya ga ba zai bi wannan doka ba yana iya ajiye aikinsa ya je ya bude asibitinsa.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyi a hirar da ya yi da manema labarai wanda aka saka a gidajen rediyoyin jihar kai-tsaye a karshen makon jiya.

A cewar Gwamnan, dole ne likitocin da ke aiki asibitin gwamnati su zabi daya, imma dai ci gaba da aiki a asibitin gwamnati ko kuma a asibiti mai zaman kansa.

“Mun san cewa aiki a asibitin gwamnati babu albashi mai kyau amma kuma akwai albarkar aiki domin akwai lada da Allah zai ba ka muddin ka yi adalci a cikinsa. Idan kana son zama Dangote ne to sai ka tafi, amma idan kana son albarka da lada sai ka tsaya a gwamnati,” inji shi.

Ya kara nanata cewa za su kira likitocin a sanar da su cewa duk wanda ya bude asibiti mai zaman kansa dole ya rufe in kuma ya zabi yin aiki asibitinsa ne sai ya bar aiki.

“Muna da labarin yadda marasa lafiya ke zuwa asibitin gwamnati domin neman magani amma sai irin wadancan likitoci su fada musu cewa cutarsu ba ta nan ba ce, don haka sai su tura su nasu asibitin wanda yin hakan ba daidai ba ne, cin amana ne,” inji shi.