✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwarzuwar ’yar wasan Afirka ta bana Asisat Lamina Oshoala dawasu abubuwa muhimmai game da ita

-Mahaifanta ba sa son ta yi kwallon kafa -Ta zama Gwarzuwar Kwallon Afirka har sau 4 -Ta taba cin ci manyan kyautuka 7 a shekara…

-Mahaifanta ba sa son ta yi kwallon kafa

-Ta zama Gwarzuwar Kwallon Afirka har sau 4

-Ta taba cin ci manyan kyautuka 7 a shekara daya

-Burinta na zama ’yar kwallo ya sa ta fita daga makaranta

An haifi Asisat Oshoala a Unguwar Okorodu dake cikin garin Legas inda ta fara sha’awar buga kwallon bayan da take kallon kungiyar kwallon kafa ta maza ta Liberpool suna wasa a talabijin. Mahaifanta suna kasuwancin gwal ne da kuma kayan sawa wannan ce ta sanya suke cike da fatan wata rana Asisat za ta zama lauya. Ita kuwa Asisat ta mayar da hankalinta wajen zama ’yar kwallo, don haka bayan an kai ruwa rana sai iyayenta suka barta ta dena zuwa makaranta ta koma kacokan tana koyon kwallo.

Asisat ta fara buga wa kungiyar  FC Robo daga 2009 zuwa 2013.  Daga nan kuma sai ta koma kungiyar RiberAngels inda ta yi wasa na kaka biyu kafin daga bisani likafa ta yi gaba inda ta samu shiga kungiyar kwallon kafa ta mata ta Liberpool dake Ingila a ranar 23 ga watan Janairu 2015.

A cikin shekara ta 2014 Asisat ta ci muhimman kyautuka har guda 7 a matakai dan-daban na kwallon kafa kamar haka

  1. Kwarzuwar ’yar wasan kwallon kafa ta Afirika
  2. Kwarzuwar ’yar wasan kwallon kafa
  3. Kyautar ’yar wasa mai karancin shekaru ta Afirika
  4. Kyautar cin kwallo ma fi shahara bangaren mata na Afirika
  5. Kyautar ’yan kasa da shekara 20 ta FIFA ta golden boot
  6. Kyautar ’yan kasa da shekara 20 ta FIFA ta cin kwallon da ya fi shahara

Haka kuma Asisat a shekarar 2015, ta ci kyautar kwarzuwar ’yar kwallon kafa BBC, a yayin da kuma a 2016 ta lashe kyautar takalmin zinari ta ’yan kwallon mata ta Afirika. A 2017 kuma ta lshe kyautar Aitero ta kwarzuwar ’yar kwallo yayin da kuma a bana ta sake zama kwarzuwar ’yar kwallon Afirika.

Wannan shi ne karo na hudu da Asisat ta ci wannan kyauta, inda a baya ta lashe wannan gasa a shekarun 2014 da 2016 da 2017. Asisat ta kafa gidauniya mai suna Asisat Ashoala wacce take taimaka wa mata matasa don su cimma burinsu na zama ’yan kwallo ko kuma wani buri wanda suke da shi sabanin wanda mahaifansu suke son su yi kamar yadda abin ya faru gareta.