✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Legas na duba yiwuwar bude masallatai da coci-coci

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu yace gwamnatin jihar na duba yiwuwar bude masallatai da coco-coci tare harkokin kasuwanci kafataninsu. A cewar Sanwo-Olu akwai bukatar daukan…

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu yace gwamnatin jihar na duba yiwuwar bude masallatai da coco-coci tare harkokin kasuwanci kafataninsu.

A cewar Sanwo-Olu akwai bukatar daukan matakin duba da mahimmancin kasuwanci da al’amuran yau da kullum a jihar, sai dai babu garaje a matakin.

Yace  jami’an gwamnatin jihar  da ke aiki a bangaren kiyaye lafiyar jama’a tare da kare muhalli za su ziyarci wuraren ibada da suka hadar da masallatai, coci-coci, bangarorin kasuwanci da suka hadar da wuraren shakatawa da samar da nishadi, da gidajen sinima, gidajen sayar da abinci, tare da masana’antu da sauransu.

Babajide Sanwo-Olu ya kara da cewa jami’an za su binciki wuraran da zasu  ziyarta domin su gane wa idanunsu yadda ake daukar matakan kare yaduwar coronavirus.

Gwamna Sanwo-Olu ya shaida haka ne a sanarwar da ya fitar bayan taron da yayi na masu ruwa da tsaki a sha’anin a sha’anin tsaron jihar, taron da ya gudana a ranar Lahadi a gidan gwamnatin jihar da ke Marina a Legas.

” Muna duba yiwuwar bude  al’amuran yau da kullum tare da yadda zamu tsara budewarsu baki daya, idan mun lura jama’a na bin matakan kare yaduwar cutar sau da kafa, zamu bada umarnin budewa cikin makwanni  biyu zuwa zuwa uku, in kuma an sami aka sin haka matakin zai iya daukar wata daya zuwa biyu.

” Sai mun tabbatar ana bin matakan kariya kafin  mu bada umarnin budewa” inji shi.

Ya kara da cewa duba da kasancewar Legas cibiyar masana’antu da al’amuran yau da kullum ba zai yuwu a ci gaba da kulle al’umma a gida har abada ba.

Tuni dai aka sassauta dokar kulle a Legas bisa matakan kare yaduwar cutar ciki har da ci gaba da rufe wuraren ibada da suka hadar da masallatai da coci-coci da wuraren nishadi tare da dokar hana fita daga karfe 8 dare, zuwa  6 na safe, da kuma dokar takaita zirga zirgar jama’a daga ciki zuwa wajen jihar ko akasin hakan.