✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haba mutanen shiyyoyin Katsina da Funtuwa!

A ranar 23 ga Satumban 1987, shekara 32 da kwana 25 da gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta kirkiri Jihar Katsina daga…

A ranar 23 ga Satumban 1987, shekara 32 da kwana 25 da gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta kirkiri Jihar Katsina daga Jihar Kaduna, bayan zaman shekara 20 cur da mutanen tsofaffin lardunan Zazzau da Katsina suka yi a zaman jiha daya da sunan Jihar Arewa ta Tsakiya, bayan da gwamnatin soja ta Janar Yakubu Gowon ta fara kirkiro jihohi a kasar nan a 1967.

Lokacin da aka kirkiro Jihar Katsina daga Jihar Kaduna, akwai kananan hukumomi 14, a tsohuwar jihar baki dayanta. Kananan hukumomi bakwai da sabuwar Jihar Katsina ta gada su ne: Katsina da Daura da Funtuwa da Kankiya da Dutsin-Ma da Malumfashi da Mani. Wadannan kananan hukumomi bakwai su ne sannu a hankali sojoji na kara kirkiro jihohi da kananan hukumomi, a yau jihar take da kananan hukumomi 34. Daga wancan tsarin ne aka raba kowace jiha zuwa mazabar dan Majalisar Dattawa uku, inda Jihar Katsina ke da mazabar dan Majalisar Dattawa ta Katsina ta Tsakiya da  Katsina ta Kudu (Funtuwa) da Katsina ta Gabas (Daura).

A zaben aniyar mika mulki  a hannun  farar hula da gwamnatin Janar Babangida ta fara a karshen 1991, Gwamnan farar hula na farko da Jihar Katsina ta zaba shi ne Alhaji Sa’idu Barda daga Katsina ta Tsakiya, yayin da Alhaji Abdullahi Garba Aminchi daga  Katsina ta Kudu ya zame masa Mataimaki, aka bar yankin Katsina ta Gabas da mukamin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, mukamin da har yanzu yake a yankin. Kada ka tambaye ni wa ya wakilci jihar a matsayin Minista, kasancewar saman sojoji ke mulki.

Waccan jamhuriyya dai ba ta kai labari ba, saboda a watan Nuwamban 1993, duk da Shugaba Babangida ya kafa gwamnatin rikon kwarya, ya sauka, Janar Abacha ya tuntsurar da gwamnatin rikon kwaryar, ya zauna kan karagar mulki har kusan shekara biyar, sai da ta Allah ta kasance Janar Abdulsalami Abubakar ya hau mulki a watan Yunin 1998, ya kuma mika mulki ga farar hula a ranar 29 ga watan Mayun 1999.

A 1999 da gwamnatin Janar Abdulsalami ta dawo da mulkin dimokuradiyya, marigayi tsohon Shugaban Kasa Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa daga Katsina ta Tsakiya shi ya zama Gwamnan farar hula na biyu a jihar, har tsawon shekara 8, 1999 zuwa 2007, Alhaji Ahmed Tukur Jikamshi da Alhaji Abdullahi Aminchi da suka yi masa mataimaka duk daga Katsina ta Kudu suka fito.

Bayan marigayi ’Yar’aduwa ya gama mulkinsa na shekara takwas, Gwamna Ibrahim Shehu Shema da ya gaje shi daga shekarar 2007 zuwa 2015, shi ma dan shiyyar Katsina ta Tsakiya ce, wadanda suka rufa masa baya, Barista Sirajo Damari (a 2007 zuwa 2011) da Barista Abdullahi Garba Faskari (a 2011 zuwa 2015), dukkansu daga Shiyyar Katsina ta Kudu suka fito. A zabubbukan 2015 da banan nan, mulkin jihar a karon farko ya zakuda zuwa shiyyar Katsina ta Kudu kuma a hannun Alhaji Aminu Bello Masari, yayin da Mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu ya fito daga Shiyyar Katsina ta Tsakiya.

Mukaman ministoci tun daga 1999 zuwa yau ana samun sabarta-juyarta a tsakanin shiyoyin uku. Alal misali a gwamnati Cif Olusegun Obasanjo 1999 zuwa 2007, an fara da Alhaji Sani Zangon Daura da Alhaji Kabir Sa’idu Daura da suka fito daga Shiyyar Katsina ta Gabas, daga bisani aka samu Alhaji Lawai Batagarawa daga Katsina ta Tsakiya. Da marigayi Alhaji Umaru ’Yar’aduwa ya zama Shugaban Kasa a shekarar 2007 zuwa 2010, Alhaji Abba Sayyadi Ruma daga shiyyar Katsina ta Tsakiya shi ya kansance Minista mai wakiltar Jihar Katsina. Bayan rasuwar ’Yar’aduwa ne, Mataimakinsa Dokta Goodluck Jonathan ya hau mulki sai ya nada Alhaji Murtala Shehu ’Yar’aduwa daga shiyyar Katsina ta Tsakiya a matsayin Minista mai wakiltar jihar. Bayan da Shugaba Jonathan ya ci zaben shekarar 2011, sai ya nada Alhaji Musa Sada daga Shiyyar Katsina ta Gabas a matsayin Minista mai wakiltar jihar ta Katsina.

Tunda Shugaba Muhammadu Buhari da ya fito daga Jihar Katsina kuma dan Shiyyar Daura ya zo kan karagar mulki a shekarar 2015, ya sake cin zaben bana, Sanata Hadi Sirika daga Shiyyar Katsina ta Gabas shi ke Minista a gwamnatin Buhari.

Mai karatu na kawo wannan dan tarihin yadda mulki ya kasance a jihar Katsina zuwa yau, don in aza ka a kan muhawarar da aka fara a daidai bikin cikar jihar shekara 32 da kirkirowa, kan cancantar lallai sai mulki ya zakuda daga shiyoyin Katsina ta Tsakiya da Katsina ta Kudu  zuwa Shiyyar Katsina ta Gabas da ba ta taba dana mukamin Gwamna ko na Mataimakinsa ba.

Amma abin ka da harka ta dimokuradiyya, mai cike da ’yancin fadin albarkacin baki, koda kuwa a kan karya ce, sai ga mutane irin su Mohammed Danjuma da ya kira kansa Kakakin Kungiyar ’Yan gaba-dai-gaba-dai Jihar Katsina yana cewa neman haka a irin wannan lokaci da mulki ya fara kankama a zango na biyu ga Gwamnatin Alhaji Masari, wai ba daidai ba ne kuma bai dace ba. Ya kara da cewa kyautuwa   ya yi Shiyyar ta Gabas ta zama mai godiya ga Allah da take da Shugaban Kasa baki daya, Shugaban da ya dukufa wajen raya yankin da ka iya zama abin alfahari a nan gaba.

Daga can ma yankin Funtuwa an ruwaito wani jigon siyasa Alhaji Bala Abubakar, yana cewa kodayake ba laifi ba ne Shiyyar Katsina ta Gabas ta nemi Gwamna a shekarar 2023, amma ya kamata mutanen shiyyar a koyaushe su zama masu godiya ga Allah da dansu yake Shugaban Kasa da kuma Sanata, abin da a ganinsa ya ce shiyyar ita ta fi kowace shiyya ta kasar nan morewa.

Ga masu irin wadannan ra’ayoyi da za ka kira na son zuciya ko rufewar idanu, sai a tuna masu cewa damar da tsarin mulkin jam’iyyun siyasar kasar  nan ya bayar na yin karba-karbar mulki a kasa da jihohi, shi mutanen Shiyyar Katsina ta Gabas suke magana a kai ba wani abu daban ba, wanda irin wadancan mutane sun san da ita sarai amma suke sukar samuwar hakan.

Don haka ko Shugaba Buhari na Shugaban Kasa, ko ba ya yi, ’yancin mutanen Shiyyar Katsina ta Gabas ce su mike tsaye su yi ta kururuwa da kiyare-kiraye ga mutanen sauran shiyoyin biyu na su ma a ba su su dana, don kuwa damarsu ce. Yin shirinsu tamkar sarayar da damar tasu ce. Batun shiyyar na da Shugaban Kasa da Sanata, wannan kuma dama ce ta tsarin mulkin kasa, shiyyar ta samar da Sanata da zai wakilci shiyyar kamar sauran shiyyoyin kasar nan, don haka ba alfarma ba ce.

Shin mutanen wadancan shiyyoyi biyu, sun manta lokacin da marigayi ’Yar’aduwa yake Shugaban Kasa, Gwamna Shema na Gwamna dukkansu daga Shiyyar Katsina ta Tsakiya suke, ba wanda ya taba kawo batun shiyyarsu daya, sai yanzu? Adalci dai shi ke zamantakewa na gaskiya. Ya kamata a saurari mutanen Shiyyar Katsina ta Gabas kan batun zakudawar mukamin Gwamnan Jihar Katsina zuwa shiyyarsu.