Search
Subscribe
Hada kan al’ummar Jos ne babban burinmu – Shehu Bala

Alhaji Shehu Bala

Hada kan al’ummar Jos ne babban burinmu – Shehu Bala

Sabon Shugaban Riko na Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, Alhaji Shehu Bala Usman ya ce babban abin da za su sanya a gaba, shi ne hada kan al’ummar karamar hukumar. Alhaji Shehu Bala ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos, inda ya ce Karamar Hukumar Jos ta Arewa kamar Najeriya ce, domin ta kunshi dukkan kabilun jihar da Najeriya baki daya. Don haka kowa yana da hakki a karamar hukumar. Ya ce yin haka ne zai kawo tabbataccen zaman lafiya da kwanciyar hankali a karamar hukumar.

“Har ila yau za mu farfado da ’yan banga ta hanyar tallafa musu, don inganta tsaro a karamar hukumar. Babu shakka idan aka samu zaman lafiya da tsaro za a samu ci gaba a karamar hukumar,” inji shi.

Ya mika godiyarsa ga Gwamnan Jihar Barista Simon Lalong kan damar da ya ba shi, ta rikon shugabancin karamar hukumar. Ya bada tabbacin cewa da yardar Allah, zai yi iyakar kokarinsa wajen ganin ya rike wannan amana da aka ba shi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin