✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadaddun kayan mar-mari da kuskus

Kayan hadi: . Abarba .  Ayaba . Kankana . Gwanda . Sukari . Filebo . Yogot . Kuskus Yadda ake yi: Uwargida za ki fara…

Kayan hadi:

. Abarba

.  Ayaba

. Kankana

. Gwanda

. Sukari

. Filebo

. Yogot

. Kuskus

Yadda ake yi:

Uwargida za ki fara soya kuskus dinki da man gyada sai ki ajiye shi a gefe. Sannan ki dauko kayan marmari ki yanyanka su kanana irin yankan fruit salad. Sannan ki hada su a mazubi guda.

Sai ki dauko soyayyen kuskus din nan ki zuba a kai. Ki zuba sukari dan kadan a ciki. A karshe sai ki zuba yogot dinki a ciki. Sai ki sa shi a firiji don ya yi sanyi.